Amfani da kaidojin VOICE dan inganta shiryen-shiryen manoma

Gabatarwa

Rediyo hanya ce ta sadarwa mai matukar amfanin a wurin manoman nahiyar Afrika. Yawancin kowa na iya kamawa ya saurara. Tana iya bada muhimman bayanai akan lokaci a yaren da mutanen nahiyar ke ji. Haka kuma Rediyo, (a wasu lokutan tare da wayoyin salula) na iya bawa manoma kakaurar murya a wurin cigaban su.

Amma Rediyo, ba wai ko da yaushe take tasiri ba. Hasali ma, shirin manoma na zuwa da gajiya wa, kamar:

  • Da kyar ake jin muryar manoma.
  • “Masana” da ake hira dasu, a bangare daya, ana girmama su ko da abun da suke fada ya taimaka ko bai taimaka ba.
  • Masu gabatar da shirin suna wulakanta manoma, wanda suke kallon su a kaskance.
  • Akwai abubuwa masu muhimanci da ake kyalewa, ko a kawar da ido saboda suna da rikitarwa, ko alamura ne da ake takatsun-tsin, ko suna bukatar karin bincike.
  • Ba’a bawa masu gabatarwa horo, sanan ana bukata su samar da shirye-shirye masu inganci ba tare da kula ko taimako ba.
  • Sanan da yawan shirin manoma basa kayatar da masu sauraro!

Sau da yawa, gidajen rediyo na tunanin cewa shirin manoma shiri ne a cikin jadawalin shirye-shiryen su da kawai zasu na “sakin” bayanai game da aikin gona, tare da tsamanin masu sauraro zasu yi amfani dashi. Amma, shirin rediyo muhimmiyar hanyar sadarwa ce ta daban, wace take da nata karfin da rashin karfi, kamar kagagen litatafi, ko litafin katun, ko kuma waka. Shirin manoma mai inganci yana bin wasu ka’idoji da suke nuna karfin gidan rediyo.

A matsayinka na mai gabatarwa, kana so shirin manoman ka ya zama mai amfani ga manoma, ya zama abun sha’awa – har ma ya zama abun karfafa gwiwa, a wurin manoma. Haka kuma, kana so ace masu sauraron ka na da yawa sosai daka dukan manoma maza da mata. Domin taimakon ka, mun hada maka wadanan “hanyoyin mafi dacewa” da kayi amfani dasu a matsayin ka na mai gabatar da shirin manoma, mun sa su a cikin rukunai da zasuyi maka saukin tunawa da saukin amfani.

Mun kira su da kaidojin VOICE dan inganta shiryen-shiryen manoma. Akwai ka’idoji biyar, wanda a turance, muhiman kalmominsu in ka hada su, zasu fitar da kalmar “VOICE”.

Munyi bayanin wadanan ka’idoji a saki layinka da suke gaba. Akwai lokuta da dama da wadanan ka’idoji suke da amfani kamar:

  • Daka farko, idan tashar rediyonka ta kirkiro shirin manoma.
  • Duk sati, loakacin da masu shirin manoman suke shirya shirin su na gaba.
  • Duk sati, lokacin da masu shirya shirin suke bitar ingancin shirin da ya wuce.
  • Duk lokacin da kake koyar da sabon mai gabatar da shirin manoma, ko tunatar dashi akan sanin makamar aikinsa.
  • Sanda kake bitar shirin ka na manoma, sai kuma.
  • Sanda tashar ka suke tara bayanan karshen shekara na shirin ka na manoma.

Idan ka na da tambaya ko abun cewa game da wadanan ka’idoji, ko kuma tambayoyi game da yadda zaka gudanar dasu a aikace, zaka iya tuntubar mu ta nan info@farmradio.org.

Kaidojin VOICE dan inganta shiryen-shiryen manoma

V: Shirin yana daraja manoma masu karamin karfi, du kuma maza da mata. Yana girmama manoma ta kokarin su na samar da abinci mai gina jiki ga iyalan su da kuma samar da shi a kasuwa, a lokuta da yawa a cikin kalubale masu girma. Yana isar manoma dan su fahimci irin halin da suke ciki, kuma ya dukufa don tallafa musu a aikinsu na noma da kuma ƙoƙarin inganta rayuwar su ta karkara.

O: Shirin ya samar wa manoma damar suyi magana a kuma saurare su akan ko wana irin al’amri ne. Yana karfafa gwiwan manoma masu karamin karfi su fadi abun da ke damun su, su tattauna akai, sanan su hadu su shawo kan al’amarin. Yana tilastawa wanda suke da hakkin taimakawa su saurare su kuma suyi musu aikin da ya dace.

I: Shirin na samar wa manoma da bayanan da suke bukata, a lokacin da suke bukatar bayanin. Manoma na bukatar wasu takamaiman bayanai kuma suna san su akan lokaci dan su dauki mataki akai.

C: Shirin ya zamanto ba fashi da kuma sauki. Ace ana watsa wa duk sati, a lokacin da manoma mata da maza zasu iya saurara.

E: Shirin ya zamanto cewa akwai nishadi, sanan ya zama abun tunawa. Ya zamanto ya jawo hankalin manoma. A gabatar da abubuwa masu rikitarwa a cikin sauki da zai taimakawa manoma suna tunawa.

Godiya

Gudunmuwa daka: Doug Ward, Ciyaman din FRI da ya wuce, an kuma yi bitan sa a cikin shekarun da suka wuce da gudunmuwa daka ma’aikatan FRI, da masu gabatar da shirin manoma a yankin sahara Afirka.

Wanan aikin an fasara shi daga tallafin da Ma’aikatar Tarayya ta Hadin Gwiwa Tattalin arziki da Cigaba ta kasar Jamus ta cikin Deutsche Gesellschaft für Internationale Zusammenarbeit GmbH (GIZ) da kuma abokiya hulda ta “Green Innovation Center for the Agriculture and Food Sector” a Nijeriya.