Yanda za’a samo kudin shigowa dan daukar nauyin shirin noma

Ta yaya samun kudin shigowa zai taimake ni in gamsar da masu sauraro na?

  • Yana tabbatar da cewa masu sauraro suna cigaba da sauraran shirin manoma.
  • Idan kudi na shigowa sosai, akwai yiyuwa mai karfi, masu sauraro zasu samu bayanai mafi inganci, akan lokaci na kuma kwarai.
  • Yana tabbatar da cewa gidajen radio suna da kudin da zasu bawa manoma dama su bayana ra’ayin su da bukatun su a yada kowa yaji.

Ta yaya samuwar kudin shiga zai taimaka mun wurin shirye-shirye masu inganci?

  • Yana sawa gidan radio ta zamo tana da kayan aiki na gari kuma na zamani.
  • Yana tabatar da cewa ana biyan masu aiki albashin su.
  • Yana tabatar da cewa gidan radio yana aiki.
  • Yana taimakawa masu rahota su fita suje su tattauna da manoma a wurin aikin su, su samo bayanai daka bakin masu sauraro.
  • Yana bawa gidajen rediyo dama su kara karfafama wadanda suka kware wurin shirin noma ilimi, ta yadda zasu kawo rahoton alamura da suke da muhimmanci ga manoma ta hanya mai kyau da nishadi.

Ta yaya zan fara?

  1. Ka mayar da samun kudi shiga abu mai muhimmanci.
  2. Kasan dokokin talla a kasar ka.
  3. Kasan masu sauraranka, ka maida masu sauraranka hanyar samun kudinka.
  4. Ka kirkiri taget mai yiyiwa.
  5. Kasan babanci tsakanin talla, daukar nauyi da kuma hadin gwiwa.
  6. Ka nemo wurin samun kudi daban-daban.
  7. Ka samar da pakiti kala-kala na talla sanan ka kirkiri kalanda ta talla.
  8. Kayi amfani da damar da gidan radiyo suka baka na yada labarai ka janyo masu talla.
  9. Kana maganar mai zasu samu in sunyi talla da kai.
  10. Ka gina dangantaka.
  11. Ka zamanto kana kare masu sauraronka.

Bayanai

1. Ka mayar da samun kudin shiga abu mai Muhimmanci:

Idan ka yanke hukuncin gabatar da shirin manoma, ka sa hanyar samun kudin shiga abu mai muhimmanci daka farko. Kasa masu tara maka kudi akan harkar!

Amma akwai kalubale samun masu talla da masu daukan nauyi shirin manoma idan masu talla da masu daukan nauyi suka dauka shirin naka bashi da farinjini.

Kuma ba masu talla da masu daukar nauyi ne kadai suke da irin wanan ra’ayin ba. Har ma masuyi maka talla a tim dinka na iya kin yarda cewa shirin noma na da farin jinni. Zaka iya dauka yafi sauki ka samu talla a cikin shirye-shirye da suke kadai-kadai da siyasa akan shirye-shiryen da suke magana akan al’amarin da ya shafi zamantakewa—kamar shirin noma ko na koshin lafiya da abinci masu gina jiki—na da muhimmanci ga kowa, kuma suna da dumbin masu sauraro. Wakilta wadanda suka fi kowa iya samo talla a aikin nemo kudin shiga zai karawa shirin ka daukaka.

Sarrafa kashe kudi

Yana da kyau a samo kudin shiga, amma idan ba’ayi taltalin su ba, samun su bashi da mafani. Ka tabbatar ka samu wanda yake da ilimin taltalin arziki ya kula ma da kudin shiga daka samu daka talaluka, daukan nauyin shiri, alumma gari, da duk wata hanyar samun kudi.

Gudanar da kashe Kudi da kyau ya hada da:

  • Ka shimfida jerin kaidojin tambayar fitar da kudi da kuma kaidojin amincewa su fita.
  • Kana yin kasafin kudin aikace-aikacen ka duk shekara ko kuma bayan watanin uku dan ka san nawa suke shiga nawa ne suke fita.
  • Kana bin didigin kudin shiga da na fita. Ka tsara lokutan da zaka na bibiya sauran ma’aikatan ka dan ka tabbatar komai na tafiya daidai.

Idan babu daya daka cikin maaikatan ka masu ilimin lissafin kudi, ka nemi taimakon gwamnati ko NGOs (kungiyoyi masu zaman kansu) da zasu taimaka maka su koyar da su lissafin kudi. Zaka iya tuntubar masu opis din lissafin kudi kayi musu talla su kuma su koyar da maaikatan ka akan kwarewar lissafin kudi.

2. Kasan dokoki da ka’idojin talla a gidan rediyo a kasar ka

Wasu abubuwa kadan da zakai bincike akai:

  • Iyakar lokacin da zaka iya bayarwa ayi talla a cikin shirin awa daya.
  • Kaidoji akan abubuwan gaskiya da cutarwa da wasu sauran kaidoji na talla.
  • Halaya akan gasa.
  • Hukunci da takunkumi akan wadanda suka karya kaidoji ko dokoki.

Ka tuna zai iya yiyuwa akwai kaidoji na kasa, da yanki/ ko jaha/ ko gari/ unguwanni, da sauran matakai.

Gidajen rediyo na alumma ana hanasu gaba daya ko wani bangare karbar kudin talla a kasashe da dama. Idan kana aiki da gidan rediyon alumma, ka tabatar kasan abun da aka yadda ayi da abun da ba’a yarda ayi ba. Gidajen rediyon alumma zasu dogara ne akan hanyoyi samun kudi bana talla ba.

3. Kasan masu sauraron ka: Ka juya sauraro zuwa kudi

Sanin irin kayan da irin ayyukan da masu sauraro ke bukata kuma suke so zai taimaka wurin sanin masu bada-talla da suka dace a shirin ka na noma. Dan ka karawa kanka damar samun talla, ka tabbatar ana gabatar da shirinka a lokacin da mata da maza suka fi sauraron shirin manoma. Idan ka gabatar da shirin ka a lokacin da mutane kadan ne suke sauraro, wanda ya baka talla ba zai ga wani amfanin baka talla ba a wanan lokacin.

Abun nufi, gidan rediyon da tasan adadin yawan masu sauraronta da yawan mutanen da suke sauraran wani shirinta tafi yin nasara wurin sayar da lokutan talla. Idan zaka iya fadama masu bada-talla da karfin gwiwa cewa in suka baka talla a shirin ka na manoma zai isar zuwa dumbun mutane, zai iya sawa su suyi pepen talla. Hakazalika masu daukar nauyin shiri, wanda za’a kira sunansu hade da shirin naka na manoma.

Ba kowace gidan rediyo bace ko kasashe ke samun masu sauraro da yawa ba, amma akwai kugiyoyi da kamfanoni da zasu iya samar da wanan akan wani kudi da zaka bayar. Ka dauki wanan kudin a matsayin jari ka zuba.

Sani da kuma fahimtar bangarorin da masu sauraro ke kama gidan rediyonka zai taimaka wurin tsari sosai. Ka tsaya kayi tunanin kamfaninnika da kungiyoyi masu daukar-nauyi da zasuyi sha’awa samun cimma masu sauraron nan.

Idan kana binciken masu sauraro, zaka so kasan:

  • Mutane nawa ne ke sauraro?
  • Su waye ke sauraro (maza, mata, shekaru, aiki, dss.)
  • Shin masu sauraro suna ji su ma wasu muhimman bangare ne acikin shirin, ko kuma biyayya kawai suke wa shirin?
  • Shin gidan rediyon na daukar bukatu da ra’ayoyin masu sauraro da girmamawa? Masu sauraro na jin cewa gidan rediyon aikin su takeyi? Idan haka ne, ta yaya?
  • Shin ana gabatar da shirin ne a lokacin da yafi dacewa da masu sauraron da masu bada talla suke son samu?
  • Masu sauraro na iya bada kudi kyauta idan shirin zai taimakawa manoma?
  • Wana irin tallan kayayaki masu sauraro zasu so suji lokacin shirin manoma?

Domin karin bayani akan binciken masu sauraro, ka duba FRI’s Yadda masu Gabatarwa zasuyi How to learn about your audience and what audience members needs from your program.

4. Ka kirkiri buri da zaka iya cikawa

Idan ka rubuta kassafin kudi domin tsarawa, shiryawa, da gabatar da shiri, mai tasiri, da tattaunawa da juna, akan lokaci, da kuma shiri dake bayani mai gamsarwa, dole ka fadawa kanka gaskia. Gidan radio nada tsayayen kudin kashewa (albashi, kayan aiki, wutar lantarki, dss), shi kuma shirin manoma yana da bukatar karin kashe kudi. Misali:

  • Maaikatan ka nasan ziyara wata alumma dan tattaunawa dasu da samo waso kayan aiki.
  • Ka tuna ka kara kudin intanet don yin bincike a yanar gizo.
  • Dole ka hada kai da maaikatar lafiya da ta gona, da wakilansu da za suna zuwa gidan radio domin tattaunawa dasu a shirinka ko amsa tambayoyi shirin waya da kuma taimakawa wurin tsara shirin.
  • Dole ka samarwa maaikatan ka wayar selula da kudin kati dan suna karbar jawabai daka masu sauraro.

Duka wanan yana bukatar kudi. Yana da muhimmanci ka lura da duk wadanan kashe-kashen kudin lokacin da kake saka wa kanka taget na samo kudin shiga. Ka kaiyade kudin talla a shirin ka akan wadancen dalilai. KA sanya farashinka yayi sama sosai dan maaikatanka su samu suyi aikinsu sosai cikin yanayi mai kyau da zaka iya basu.

Idan zaka sami mai bada talla, ka tabbatar abun da kake nema a wurinsa yayi daidai akan abun da zasu iya biya. Idan farashin ka yayi tsada da yawa, ko kuma ka tashi siyar da pakiti da yayi girma, zaka iya rasa abokan ciniki. Ka kintata nawa zasu iya biya a talla sai ka tsara gabatarwa akan wanan kudin da zasu iya biya.

5. Kasan banbanci tsakanin talla, daukar nauyi da kuma hadin gwiwa.

Talla: Harka cinikayya ce kawai: ka biya a baka fili a gidan radio

Daukar Nauyi:

  • Zai iya yin tasiri akan dangantaka ka da masu sauraro. Idan masu sauraro suna son mai daukar nauyi kuma sun yarda dashi, zasu iya dora wa tashar ka wanan son da suke yiwa mai daukar nauyi shirin. Wanan yana karawa mai daukar nauyi daraja da kuma gidan rediyon, zai sa a ringa kallon mai daukar nauyi a matsayin mai kishin kasa na gari.
  • Zaka iya banbance mai daukar nauyi tsakanin sa da abokan kasuwancin sa.
  • Zai iya hadawa da kudi, amma bashi kadai bane. Misali, zaku iya musanyan fili a gidan rediyo da wasu ayyuka da gidan rediyon take bukata.
  • Yafi dadewa akan talla.

Hadin gwiwa: Anfi yinsa da kungiyoyin masu zaman kansu da wasu kungiyoyin da suke aiki a harkar lafiya, ilimi, noma, ko kare hakkin dan-adam. Kamar daukar nauyi, hadin gwiwa ba dole bane ya kawo kudin shiga, amma saboda wadanan kungiyoyin zasu iya maka wasu aiyukan, zasu rage ma kasha kudin ta wani bangaren.

Tallafin Alumma:

  • Zai iya hadawa da gudunmuwa daka wasu mutane.
  • Duka maaikata zasu iya shiga. Misali, mai gabatrwa zai iya halartar taro da alumma suka shirya, manyan maaikatar tashar zasu iya shiga wani kungiyar hadain kan alumma, ko agaji, ko cinikaiya, ko komitin koli, haka kuma sakatariya zata iya rika yin waya dan ta sabunta memba.
  • Za’a ringa karbar kudin kungiya duk wata a madadin satifiket na taimakon yan kasuwa masu karamin karfi ko kungiyoyi, ko mutane. Yawanci, tashar zata ambacin sunan dan kungiya a shirinta ta gode masa da taimakon da yake bayarwa. Wanan zai taimakawa kananan yan kasuwa, a misali, masu dinki da suke aiki ba’a gida ba, da kuma kunyiyoyin manoma, dss. Tallafin alumma na iya samar da kudin shiga sosai, musamman kananen gidajen rediyo da suke kauyuka.

6. Ka duba hanyoyi daban-daban na samo kudin shiga

Yana da muhimanci ka duba hanyoyin samun kudin shiga a wurare iri-iri saboda kar shirin ka ya dogara da yan wuri kadan. Ka duba wadanan hanyoyin:

  • Shirin bayar da gudunmuwa ko gabatar da shirin tara kudi daka gudunmuwa.
  • Taimako da alumma ke bayarwa. Ka tabbatar tashar ka tana shiga alumma ayi abubuwa da ita sosai, kuma alumma su sani. Zai fi sauki ka tunkaru mutane ka nemi kudi.
  • Kana sayar da labarai da tashoshin kasa ko na yanki.
  • Bani in baka: Misali, wani kamfani zai iya samar ma intanet ko gyaran kayan aikin ka, kai kuma ka bashi filin tala kyuata ko damar dauka nauyin wani shiri.
  • Ka nemi taimakon NGO (kungiyoyi masu zaman kansu) ko masana wurin neman kudin gudunmuwa.
  • Neman kudi ta shirye-shirye kamar kiran suna da mai gabatrwa zai nayi, ko sanarwar murnar ranar haihuwa, da kuma sanarwar mutuwa.
  • Samun talla da maaikatun gwamnati da yan kasuwa, kamar sanar da alumma muhimman abu.
  • Kananen yan kasuwa: Zai fi kawo kudi idan manyan kamfanoni ne suke baka talla, amma ba ko da yaushe yake samuwa ba. Amma yan kananan kamfani na da yawa fiye da manya.
  • Ka sayar da takarda zama memba ga masu sauraro, sai ka bawa wanda suka siya kyauta, kamar iri na shuka daka mai bada-talla, ko riga mai dauke da tambarin rediyon.
  • NGOs da suka nuna shaawar amfanin da gidan rediyo su cimma burin su.
  • Bada hanyar filaye da ba’a amfani dasu a cikin gidan rediyon.
  • Idan kaje neman tallafi ko ‘kudin aiki’daka masu bayarwa, kar ka dau alkawarrukan da baza ka iya cikawa ba, ka fadi abun da zaka iya, dan dole zakayi bayanin yadda kayi da kudin daka karshe.

7. Ka samar da pakiti iri-iri ga masu talla sanan ka kirkiri kalandar sayar da talla

Yafi kyau ka samu hanyoyi da yawa na tunkara masu talla. A maimakon su dau nauyin shirin gaba daya, zaka iya basu damar daukar wani bangaren na shirin, misali, bangaren yadda kasuwanni suka kaya ko bangaren hasashen yanayi, ko kuma bangaren amsa waya a cikin shiri. Haka zalika, idan masu talla suna da sha’awar daukan nauyin wani shiri daban ko kuma san talla a lokutan da aka fi sauraro, zaka iya musu raggi suyi talla a shirin manoma.

Kalandar talla da lokuta na musamman a shekara: Ka tuna lokuta da mutane suke kasha kudi sosai a shekara, misali bikin kirsimas ko bikin sallah. Ka tsara kalandar sayar da talaluka dan tunawa maaikatan ka suyi wa mutane Magana kafin wanan babar ranar. Samun wanan kalandar—ko a yanar gizo ko kuma a liqe a bango— zai tamaka maka tsara gidauniya tara kudi. Zaka iya kirkira pakiti na musamman na talla na wadanan lokutan a shekara. Ta wanan hanyar ne, zaka iya kunkara masu bada talla da pakiti kala-kala a shekara. Zaka iya yin jerin sunayen masu bada talla da yayi daidai da alamuran. Wanan zai tabatar da cewa kana tunkara masu bada talla da kofar shiga a talla. Zaka kuma iya cigaba da rike abokantaka da wadanda sun riga sun baka talla, kana basu garabasa da zai taimakawa wa talalunkan su.

Ka sanya adireshi yanar gizo da dandalin sada zumunta na zamani: Idan kana da shafin yanar gizo ko kuma kayi karfi a dandalin sada zumunta, ka sanya adireshi da kuma shafuka dandalin sada zumunta ka a pakitin da kake bawa masu bada talla. A misali zaka iya bada pakiti da ya kunshi yadawa a dandalin sada zumunta na Whatsapp da ya kunshi adireshin shafin mai bada talla a yanar gizo da mutane zasu bi su karanta.

Ka shiga duk wani taron alumma: Idan gidan rediyo ta shiga wani babban taro da alumma sukeyi kamar ranar manoma, tana bawa masu talla damar a sansu sosai. Masu bada talla da masu daukar nauyin shirye-shirye zasu iya, a misali daukar nauyin tashar ta buga babbar fosta da ta dauki tambarin mai bada talla da kuma hoto ko sunan abun da yake siyarwa a taron.

Ka kirkiri katin farashi: Samar da katin farashi nada amfani. Zaka iya fara ciniki akan tsayayen farashi, ya danganci kwastoma, zaka iya bada farashi ko pakiti daban. Katin farashi na sa irgan farashi yayi sauki. Farashi ya zamanto yayi laakari da masu sauraro, wata irin tasha ce, da kuma waye mai bada tallan. A misali, tashar alumma, baza ta karbi kudi daidai da tashar kasa ko ta yanki ba. Tallan babban kamfani na waya ba zai zama kudi daidai da tallan dinki ba.

Wanan wasu jerin abubuwa ne da zaka sa a cikin katin farashin ka:

  • Tsawon lokaci: Sati ko wata nawa ne zaayi ana tallan.
  • Sau nawa ne za’a sa tallan a cikin pakitin.
  • Lokacin talla: a wana lokaci ne za’a yada tallan da kuma farashin ko wana lokacin—a misali, da Safiya, ko yamma, tsakiyar safiya, lokacin cin abincin rana, da yamma lokacin komawa gida, da daddare.
  • Ambatar sunaye daka bakin DJ (mai gabatarwa) da lokutan.
  • Zabi na tsawon lokacin tallan, misali, sekon 7 a X shillings, sekon 15 a X kwacha, sekon 30 a X cedis.
  • Shirye-Shiryen da kake so a dau nauyi: ka hada da sunan shirin da lokacin da ake gabatar dashi.

Kayi bitar wanda suka baka talla ka fahimsi lokutan da suke siyan talla da kuma dalilin da yasa suke siya. Wanan zai taimake ka ka tsara yadda zaka kara tunkara su, da kuma yadda zaka tunkaru wasu masu manufofin iri —daya ko kuma manufofi —daban.

8. Ko dau damar da gidan rediyon suka baka ka janyo masu talla

Ka yada cewa akwai filin talla dan masu bada talla su sani. Wanan zai sa masu bada talla sun san cewa inde suna jin sanarwan nan, toh mutane ma zasu najin tallan su in sun bayar. Ka kirawo masu bada-talla suyi magana da maaaikatan ka na bangaren sayar da talalluka suyi tattauna.

Kayi amfani da damarka ta hanyar yada shirin ka gaba daya ranar. Idan mutane da yawa suka san kana da shirin manoma, lokacin da ake gabatarwa da kuma abun da shirin ya kunsa, mutane da yawa zasu saurara. Zaka iya daukaka shirin ka ta fosta, ziyara unguwanni, da kuma kacici-kacici. Wannan zai samar da karin masu sauraro, kuma dama hakan kowa yake so—masu bada tallan, gidan rediyon, da masu sauraro. Ka dau talla a matsayin jari a shirye-shiryen tashar ka da kuma maaikatan ka.

9. Kayi maganar mai zasu karu dashi a ciki

Kafin ka kusanci yan kasuwa da masu bada talla, kayi tunanin abokan sana’arsu da suke gasa. Ta yaya talla a tashar ka zai daura su akan abokan gasar su? Kayi Magana akan burin su da kuma yarda zasu cimmusu. Suna san kwastomomi da yawa, suna san tallata hajarsu, su gina soyayya a zukatan kwastomominsu? Mai suke tunanin rediyo za tayi musu? Amsoshin wadanan tambayoyin sune zasu baka damar samar da bayanai da zai taimaka muku duka dakai da su masu talla. Haka ma masu daukar nauyi zakayi musu.

Shirin manoma yana zuwa ga masu sauraro da yawa. Amma, abu mafi muhimmanci, shirin zai iya kula dangantaka mai aminci tsakanin sa da masu sauraro. Aminci,shine muhimmun abun ga masu bada-talla, saboda masu sauraro zasu dau yardar da sukayi wa shirin su dora kan hajjojin da ake talla. Domin tsare wanan amincin, dole gidajen rediyo su bi tsari da ya hada da kaidojin talla, daukar nauyin shiri, da kuma hadin gwiwa. Lokacin da kake duba mai bada-talla ko mai daukar nauyi, ka tambayi kanka in ambatar sunan mai bada-talla yana da muhimmanci a wurin mai sauraro.

Ka gayawa sabin masu bada-talla da daukar nauyi cewa shirinka na manoma yana raba bayanai ga manoma, sanan yana zama majalisa manoma su tattauna abubawan da ya shafe su kuma yake damun su. Wasu masu bada-talla da daukar nauyi zasu so suyi mu’amala da shirinka saboda masu sauraro sun danganta shi da gaskia da rikon amana. Kayi tunanin mai yasa masu sauraro suke suarara shirinka da kuma mutunta shirinka. Sai kayi wa yan kasuwa da kungiyoyi bayanin dalilan da yasa ya kamata suyi mu’aamla da shirin ka ta hanyar talla ko daukar nauyin shirin, ko wani bangaren na shirin.

Idan ka nufi masu bada-talla, masu daukar nauyi, ko hadin gwiwa da sauran su, yana da muhimanci kayi hangen bukatunsu. Ka basu bayanai akan gidan rediyon ka, ka basu samfurin pakitin abun da kake sayarwa, har ma da takarda ko kuma rekodin din talla da aka taba sawa a tashar ka. Kasan mai kake nema ga masu bada-talla, masu daukar nauyi, da masu hadin gwiwa, ka fada musu mai za su samu daka ciki.

Hanya mafi kyau ta karfafa gwiwa yan kasuwa su dauki nauyin shirinka shine ka fada musu taimakon noma zai taimaka wurin kasuwancin su ya bunkasa. Misali, idan kamfani mai bada kaya ya dauki nauyi shirin manoma da ya taimaka musu suka ci nasara, wadanan manoman za su na siyan kaya a wurin sa.

10. Ka gina dangantaka

Ka kasance ka cigaba da mu’amala da masu bada-talla, daukar nauyi, hadin gwiwa da kuma alumma gari. Wanan zai taimaka wurin kula yarda da amintaka da gidan rediyo, ya kuma taimaka kayi aikin cikin sauki. Kayi magana da abokan huldar ka akan yadda cinikayya talla ta kasance, don kasan a ina zaka kara himma, ka tambaye su ko talla a tashar ka yayi musu tasiri, ko yasa sun samu ciniki da yawa, ko wani abu ya cenja tunda suka fara aiki da kai, sannan ko duka bangaren biyu sun mutunta yarjejeniya dake tsakanin su.

Idan zai yiyu, ka ware mutum daya daka cikin ma’aikatan ka ya zama shine alhakin hada hulda da kungiyoin masu zaman kansu yake hanun sa. Wanan ba wai dole yana karkashi bangaren masu talla bane a tashar ka, dan rike mu’amala da kungiyoyi masu zaman kansu na bukatar karin ilimi da sanin makamashin aiki daban da na talla. Saboda daukar nauyi da hadin gwiwa daban da talla, zai fi bada ma’ana idan kana da maaikaci da yake da masaniya akan irin wanan huldar dan acimma buri daya.

Idan ka hada kai da NGO dan ka taimaka musu su cimma burin su, ka tabbatar ka ajiye maaikaci daya (mislai, mai gabatarwa ko mai daukan nauyin shirin) ya zama shine alhakin hadin gwiwa yake hanun sa har karshen rayuwa hadin gwiwa.

11. Ka zamanto kana kare masu sauraronka

Tushen shirin manoma shine kare hakkin manoma masu sauraro. Wanan yana nufin kada masu bada talla suna juya akalar shirin. Misali, idan kamfani mai bada abubuwa, da yake tallata takin zamanin wani kamfanin, ya dauki nauyin shirin manoma ko yake talla a cikin shirin, idan shirin ya bada shawara ayi amfanin da takin zamanin wanan kamfanin bai ambaci sunan wani kamfani ba, wanan misali ne na mai bada-talla yana so ya juya raayin shirin ta hanyar da bata dace ba. Haka kuma, idan masanin gona ya bada shawara amfani da kamfanin takin zamani tare da sauran kamfaninnika, wanan bai zamanto hanya ta juya akalar shirin ta hanyar da bai dace ba.

Kare mutuncin gidan rediyon—anan yana nufin kin bari kudaden talla su juya ra’ayin shirin ta hanyoyin da basu dace ba—na taimakawa masu sauraro su yarda da shirin ya kuma gina biyayya. A yayin da yawan masu sauraro ya karu, mutane da yawa zasu ji talaluka kanka, wanda zai taimaki mai bada-talla. Amma ka tuna fa, tushen shirin ka shine masu sauraron ka, ba, masu bada-talla ba. Wanan yana nufin ka zama idanuwa da kunuwan masu sauraranka—da kwakwal warsu.

Ka zamanto sai ka zabi nau’oin tallukan da zakayi a shirin ka. Shirin manoma na kara daukaka kula da lafiya da inganta rayuwa manoma, iyalansu, da kuma alummar dake kauyuka. Ba kowa na talla ne ke daukaka wadancen abubuwan ba, saboda haka ka zabi masu bada-talla da hikima.

Rubuta manufofin shirin ka zai taimaka ma wurin tabbatar da kabi hanyoyin da suka dace kuma suke karfafa ma gwiwa. Zaka iya amfani da bayanin manufofin shirin ka kana saita ayyukan maaikatan ka, kuma yana da kyau kayi amfani dashi wurin takaita shirin naka, tare da cimma makusudai daka sawa shirin, da kuma amfani dashi wurin bayanin falsafar shirin gaba daya ga masu bada-talla, tare da masu daukar nauyi, da masu hadin gwiwa, da alummar unguwanni.

Domin Karin bayani akan kaidojin shhirin ka, duba FRI Yanda Mai Gabatarwa Zaiyi akan FAIR Standards (Adalci da daidaito, Daidai-wa-daida, Mutunci, Girmamawa.)

A Karshe

Ka tuna cewa, burin ka shine gabatar da shirin manoma mai tasiri, da tattaunawa da juna, akan lokaci, mai amfani, da kuma shiri dake bayani mai gamsarwa ga manoma. Shirye-shirye masu inganci na kwarai zasu janyoma ma su sa hannun jari. Idan ka na yanke hukunci akan talaluka baka sa masu sauraro a ranka, akwai hadarin cewa zaka dau hukuncin da bai dace ba. Ka sa alumma da kake wa aiki a ranka, da kuma ingancin aikin ka. Ka yarda da shirin manomanka sai masu bada talla, da daukar nauyi, da masu hadin gwiwa su yarda dashi suma.

Aina zan iya samun karin ilimi akan hanyoyin samun kudin shiga

AMARC, 2000. The African Community Radio Manager’s Handbook: A Guide to Sustainable Radio. http://www.amarc.org/documents/manuals/The_African_CR_Manager.pdf (369 KB)

Audience Dialogue website: http://www.audiencedialogue.net/

Community Radio Toolkit website, undated. The Business of Community Radio. http://www.communityradiotoolkit.net/the-business/business-community-radio/

Developing Radio Partners, undated. Guidebook on Sustainability. https://docs.wixstatic.com/ugd/4ba0ec_181def584ca64a9a9d547964fb448b0f.pdf (2.7 MB)

Fairbairn, J., 2009. Community Media Sustainability Guide: The Business of Changing Lives. Internews Network. https://www.internews.org/sites/default/files/2017-08/InternewsCommunityMediaGuide2009.pdf (3 MB)

Hughes, S., Eashwar, S., and Jennings, V.E., 2004. How to get started and keep going: A guide to Community Multimedia Centres. UNESCO: http://unesdoc.unesco.org/images/0013/001346/134602e.pdf(2.4 MB)

Mdlongwa, F., editor, 2007. Revenue Generation for Robust African Media: Practical Ideas, Experiences and Innovations of Frontline Managers. Konrad Adenauer Stiftung. https://www.ru.ac.za/media/rhodesuniversity/content/spi/documents/kas_13964-1522-2-30.pdf (1.9 MB)

Mindtools.com, undated. Crafting an elevator pitch: Introducing your Company Quickly and Compellingly. https://www.mindtools.com/pages/article/elevator-pitch.htm

Subba, B., Chapagain, Y., and Mainali, R., 2006. Community Radio Collective Marketing Strategy. Radio Knowledge Centre/Community Radio Support Center (CRSC). Nepal Forum of Environmental Journalists. http://www.amarc.org/documents/manuals/CR_Collective_Marketing_Strategy1.pdf (386 KB)

Tabing, Louie, 2002. How to do community radio: A primer for community radio operators. UNESCO. http://unesdoc.unesco.org/images/0013/001342/134208e.pdf (417 KB)

Fassara

Kamfani dan kasa: Yarda cewa wani kasuwanci, ko kamfani, ko kuma kungiya da take cinikayya, tana da haki ta zamantakewa, aladu, da kuma muhalli akan alumma da yake aiki, haka zalika kuma masu hanun jari acikinsa da kuma masu ruwa da tsaki.

Rediyothon: kamfen ne da ake gabatarwa a gidan rediyo, wanda yake dauka awa 24 ko sama da haka, dan a Tarawa gidan rediyo kudi, ko sadaka, ko kuma wata kungiya, daka masu sauraro dake bugo waya suna yin alkawarin yin kyauta, wani lokaci akan musayar kyauta.

Yabo

Mai bada gudunmuwa: Sylvie Harrison, Shugaban Tawagar Cigaban Radio Craft, Farm Radio International; Vijay Cuddeford, Manaja tantance ayyuka, Farm Radio International

Wanan labarin an dauki gudunar dashi ne daka tallafin USAID’s New Alliance ICT Extension Challenge Fund, ta hanyar International Fund for Agricultural Development a kasar Tanzania. Domin Karin bayani akan gidauniyar, ka duba: https://www.ifad.org/

The translation of this resource was carried out with the aid of a grant from The Deutsche Gesellschaft für Internationale Zusammenarbeit GmbH (GIZ) implementing the Green Innovation Centre project in Nigeria.