Yanda Zaka gamsar da Mata Manoma sosai
Da Bana gamsar da duka Mata da Maza Manoma sosai ne?
Shekaru aru-aru da suka wuce, shirye-shiryen manoma na gidan radio yafi gamsar da bukatun manoma maza. Maza masu gabatarda shirye-shirye sunfi tattauawa da masana maza akan shuka da maza sukeyi da dabobin da maza ke kiwo.
A yau munsan mata na aikin gona kamar yadda maza sukeyi a kanana gonaki. Kuma suna ciyar da iyali, su kula da yara da tsofafi.
Saboda haka mata na da mahimmanci wurin rayuwa da cigaban iyali manoma. Haka shiyasa shirin gidajen radio wanda ya kamata su gamsar da kananan manoma ya dace su gamsar da bukatun manoma mata da manoma maza suma.
Kayi nazari. Shin kana gamsar da manoma mata sosai? Duba shawarwari a kasa ka gani, guda nawa kake amfani dasu acikin shirin ka. Sai Kuma ka aiwatar da duka wadanda zaka iya.
Ta yaya wanann hanyoyin zasu taimaka mun na gamsar da masu sauraro na sosai?
- Mata manoma zasu samu bayanai da suke nia suyi noma sosai.
- Mata manoma zasu samu dama su fadi ra’ayoyinsu akan abubuwa masu muhimmanci da ya shafe su.
- Mata manoma zasu fi jin dadin shirinka.
- Maza manoma zasu san abubuwan da suka fi wa mata manoma muhimmanci, kuma zasu na la’akari da abubawan a gaba.
Ta yaya wanann hanyoyin zasu taimaka mun wurin shiryawa da kuma gabatar da shirye-shirye da suka fi kyau?
- Zasu bani shawarwari a bayyane akan yadda zan janyo da kuma gamsar da mata manoma masu saurarona na kuma gina yawon su.
- Zai bani sababun hanyoyin da zan karfafa daidaita hakkin maza da mata a gidan radio da nake.
Ta yaya zan fara?
- Ka bawa mata manoma girman da ya kamata.
- Ka gano mene yake da mahmimmanci a wurin mata, kayi rahoto akai.
- Ka yada shirin a lokacin da mata manoma zasu saurara.
- Ka karfafawa mata manoma gwiwa suyi magana a gidan radio.
- Ka tabbatar kafar gidan radion da kake na kyakyawan laakri da hakin maza da mata.
Bayanai
1. Ka bawa mata manoma girman da ya dace
Kamar yadda muka fada a sama, mata ke yawan ayuka a kananen gonaki. Kuma sunayi ne a lokacin da suke kula da jarirai, yara da kuma manya. Aikin su na da matukar mahmmanci wurin cigaban gonar iyali. Akan duk abubuwan da zakayi. Shiryawa ne, tattaunawa ne ko gabatarwa- ka tabbatar ka isar da wani sako na girmama mata dake aiki tukuru, suke daukar muhimman hukunce hukunce akan lafiya da walwalar iyalinsu, amma yawanci su na dauke da takaicin nuna wariya jinsi da ake musu. A karshe, ka tabbatar kana lura da yadda tattalin arziki daban-daban na mata da maza ke tasiri a unguwa da kuma gidaje.
Misali:
- Ka gabatar da mata a matsayin manoma, ba wai matan manoma ba.
- Kayi Magana dasu kana kiran sunan su-suma mutane ne masu zaman kansu.
- Ka tambayi ra’ayinsu akan muhimman abubuwan noma. Zasu baka mamaki abun da suka sani.
- Ka dunga bayar da labarai masu fa’ida dake nuna rawa da mata da maza ke takawa daban-daban, a misali, mata dake shuka amfanin gona na sayarwa ko kuma maza dake daukan hukunci akan abun da ya shafi lafiyar iyali.
2. Ka gano abun da yake da mahimmanci a wurin mata, kayi rahoto akan sa
A al’adance, muna tunani noma aikin karfi ne da maza kadai zasu iya. Su kuma mata suna kula da lambun ganyayaki. Amma mata sun damu kuma suna shiga duk alamuran noma da ya shafi lafiyar iyalinsu, hade da yawa ko ingancin girbin amfanin gona. A misali:
- Yanda za’a kara wa kasar noma armashi
- Lokacin da yakamata a sayar da Saniya
- Yanda zaa karawa amfanin gona ingantatun sinadirai
- Yanda za’a karbi bashin kudi dan kara yawan shuke shuke
- Yanda za’ai tanadin kudi sai lokacin da iyali ke bukata
Kaje kauye kayi taro da mata. Ka tambaye su wadana alamura suke fuskanta a aikin su na noma. Ka basu wasu daga cikin maudu’in da muka fada a sama, kar suyi tunanin batun lambu kawai ake. Ka saurare su da kyau, sai a karshe, ka gaya musu kaji abun da suka fi damuwa dashi. In kadawo dakin labarai, kayi tunanin hanyoyin da ya dace ka yi rahoto ka yada a radio.
3. Ka yada shirin a lokacin da mata manoma zasu saurara
Zaka iya shirya shiri mai kayatarwa, da zai matukar amfani mata, amma idan ka yada shirin a lokacin da mata da yawa basa kusa da radio su, shirin naka ya tashi a banza. Idan kaje kauye kana hira da mata, ka tambaye su lokacin da zasu iya jin shirin manoma a radio. Kayiwa maza irin tambayar suma. Idan duka manoma maza da mata zasu iya sauraro a lokaci daya, sai kayi shirin manoma daya da zai gamsar da duka mata da maza. Amma, idan mata baza su iya sauraro ba lokacin da maza suke sauraro, ya zama dole kayi shirin manoma sau biyu a sati, saboda duka manoman su samu. Dole hakan zaiyi wahala idan shirin naka ana bugo waya, wanda dole kai tsaye akeyi. A irin wanann yanayin, dole ka sanya bangaren kiran waya sabo a yayin da kake maimaita shirin. Mafi sauki shine, ka shirya shirin manoma daban daban guda biyu duk sati, daya na manoma mata, daya na manoma maza.
4. Ka karfafawa mata manoma gwiwa suna magana a gidan radio
A al’adu da yawa, mata na komawa baya ne, su bar maza suyi Magana akan abunda ya shafe su, na matansu da kuma iyalinsu. Amma lokaci na canjawa. Mata na da yanci suyi magana akan kansu. Al’umomi zasu fi lafiya da inganci da kuma cigaba idan ana bawa mata dama ana saurararan su, ana kuma daukan maganganun su daidai da na maza akan alamura masu mahimmanci. Ka gano inda mata suke magana hankalin su a kwance, wata kila a gidajen su, ko kuma a gona, ko kuma cikin kawayensu, ka kai musu ziyara wurin. A wanann hanyoyin, zaka samu muhimman abubuwa da zai karfafawa mata gwiwa suna magana a gidan radio. Wanann ya hada da:
- Nian mata da suka iya magana a gidan radio hankalin su kwance
- Tattaunawa da mata acikin rukunin su
- Kyale mace tayi magan a boye a yanayin da ya kamata
5. Ka tabbatar kafar gidan radion da kake na kyakyawan laakari da hakin maza da mata
Akwai hanyoyi da yawa da masu sauraro zasu gane ko kafar gidan radio na kyakyawan laakari da bawa mata hakki daidai da maza. Duba jerin abubuwa nan:
- Kana gayyatar mata su ziyarci gidan radion da kake alokacin da yake da tsaro suyi tafiya?
- Akwai ban dakin mata da yara mata?
- Shin kowa a gidan radio yana bawa mata da maza daidai girman da ya dace?
- Shin masu sauraro suna jin mata masu gatabatarwa nayin abubuwa iri-daya da wanda maza sukeyi? (Yawanci kafafen gidan radio dayawa ba sosai suke da shirye-shirye da mata ne ke jagoran ta ba)
- Shin kafar gidan radio da kake nada wani rubutacen kaidoji na bawa mata hakki daidai da maza, kuma suna aiwatar dashi kuma kowa na bada gudumuwar haka?
Sauran Muhimman abubuwa wurin gamsar da mata manoma sosai
Kayi amfani da wayan kira daban na mata masu bugo waya
Mafi akasari, mata kadan ke samun waya salula. Saboda haka idan maza ne keda kaso 90% na wayar salula, kaga kenan kaso 90% na wanda zasu kira waya a shirinka maza ne. Amma idan kana da layi daban na wanda mata zasu na kira, zaka dunga iya chan-chanjawa tsakanin layikan biyu, kenan kaso 50% wanda zasu kira waya mata ne! Duk da dai zaici kudi, kuma zaka dunga tantancewa dan tabbatar da mata ne kawai suke kira, wanan itace ingantaciyar hanyar da shirinka zai sa mata suji bayaninsu da ra’ayoyinsu na da muhimmanci.
Ka futa ka hadu da mata manoma
Ka shirya tafiya dan futa ka hadu da mata acikin unguwanni manoma. Ka yada shirin a radio dan mutane su halarta da yawa. Idan kai namiji ne, ka taho da mace mai gabatarwa tare dakai. Wanann zai iya sanya wa wasu matan su saki jiki suyi magana da kai sosai.
Ka samo mata wanda zasu saki jiki suyi magana a radio
Idan ka samo mace wace zata saki jiki tayi magana a radio, kuma tana da muhiman ra’ayoyi da zata gabatar, ka karbi lambar wayar ta ka kira ta kuyi magana akan al’amura da yawa. Wanann zai harzika sauran matan suna magana a shirye-shiryen ka na gaba.
Ka tattauna da mata acikin rukunai
Idan ka tatauna da mace ita kadai, zata iya razana ta ganin cewa kai masani ne. Amma, in ka tattauna da rukunan mata, komai zai canja. Mata suna jin wani karfi in suna da yawa. Idan daya tayi magana, wata zata iya jin zata iya karin bayani sosai akai. Sanan ta ukun zata ji zata iya ginawa akan bayanan sauran ta kara dogon sharhi akan alamarun.
Ka samar da wayar salula ga matan a wasu kauyukan
A wasu kauyukan, ba macen da take da waya. Idan zaka iya, ka bawa mace daya waya da dukan sauran matan kauyen zasu iya amfani da ita su kira gidan radio.
Ka gabatar da shirin rayuwa mata manoma da kuma kwarewar su
Kowa nasan jin labari da yayi kama da labarin rayuwarsa. Ta yaya wasu suka shawo kan kalubale da muke fuskanta. Me yake sa su farin ciki da bakin ciki? Ka tattauna da mata manoma su bayar da labarinsu ka yada a gidan radio. Wanann zai karfafawa wasu matan da suka fuskanci irin wadan nan kalubalen.
Haduwa da kungiyoyin mata
Ka samo kungiyoyin mata, ka gayace su, suna sauraran shirin ka, sanan suna baka sakamakon yadda shirin ya biya musu bukatun su a matsayin su na manoma. Dan Karin bayani akan kungiyoyin sauraro danna nan.
Kayi amfani da kalmomin noma na mata
A wa’yansu wuraren, mata na amfani da wasu kalmomi na daban domin su bayana sunayen wasu amfanin gona ko yadda ake noma. Wadan nan kalmomin ba ko da yaushe mai gabatarwa ya sansu ba, ko masana noma maza-ko mata manoma. Kayi amfani da kalmomin da mata zasu gane.
Ka kyale mace tayi a boye a inda ya kamata
Idan mace ana musguna mata ko ana nuna mata wariya a wurin aiki ko a gida, amma tana tunanin sakamako mara kyau idan ta fadi labarin ta kuma aka ganeta, ka taimaka mata ka isar da labarin ta ga masu sauraro. Indai har kasan sunan matar kuma ka yarda da mutuncin ta, ba sai ka yada sunanta ba ko kuma wani bayani daza a gano ta. Zaka iya canja murya ta, ta hanyar kara wa muryar gudu ko rage mata gudu da na’ura kumputa. Ko kuma kawai ka bada labarin ta ba sai ka kira sunan ta ba. Zaka iya samun labarin ta daka bayar, ya taimakawa wasu mata dayawa sun bada irin wanann labarin daga rayuwar su. Zai taimaka musu, kuma kaima zai taimaka maka matsayin ka na mai gabatarwa ka fara gano bakin zaren al’amuran. Ka tuna ba wai kawai boye sunan ta da muryar ta ke da mahimmanci ba, har ma duk wani bayani da zai iya sawa a gano itace zaka boye.
Mata manoma masana ne suma!
Wadansu manoma mata sun san yadda ake shuka kamar yadda masana suke bayani a gidan radio. Ka watsa wanann tattaunawa da wadan nan mata. Bayanan su zaiyi amfani ga manoma sosai, kuma irinsu zasu taimakawa dukan mata su gane cewa mata na da muhimmanci a harkar noma.
Ka canja yanda kake tattaunawa da maza manoma da masana maza
Idan masani na bayanin yadda yiwa Saniya rigakafi zai taimakawa maza, ka tambaye shi tayaya zai taimakawa mata manoma da iyalin su suma. Kuma ka tabbatar ka gano ko mata zasu iya samun rigakafin kamar yadda maza suke samu.
Kar kai hira da mata akan shuke shuken lambun su kawai
Da gaske ne mata su suke duka ayyukan kayan ci na lambu. Amma suma suna damuwa da dukan noman da ake a gidajen su. Kuma suna da ra’ayi kamar lokacin da yakamata a siyar da Saniya ko amfanin gona, ko kuma lokacin da zaa kara wa kasa taki, ko kuma ya dace a ci bashi dan siyan kayan aiki.
Ka koyawa mata yadda zasuyi amfani da waya salula
Wadansu matan basu samu daman koyan lambobi a makaranta ba. Ko suna da waya, basu san yadda zasu danna lambobin da suka dace ba. Ka kir-kiri hanya tunatarwa mafi sauki da zai koyawa mata lambobi a yaren da zasu gane. Ka gwada akan daidai kun mata ka gani ko ya taimaka musu, kuma Idan yayi, ka dunga yada wanan nasara akai akai.
Wanann misali ne na tunatarwa a saukake da zaka iya fassarawa ka maida shi waka. Zaka iya samun wanda yafi wanan. Zai iya yiyuwa kamfani wayarka ya samar da irin wanann hanyar tunatarwa da zaka iya amfani dashi. Ka yada shi lokacin da ake zuwa hutu a shirinka na gidan radio gaba daya cikin sati. Ka tambayi mata ko ya taimaka musu.
Da wayar salula ki
Zaka iya magana da kowa a duniya
Kawai zaki san
Wadana lambobi zaki danna
Gasu nan, daga hagu zuwa dama:
– layin sama: daya, biyu, uku
– layi na biyu: hudu, biyar, shida
– layi na uku: bakwai takwas tara
-layi na kasa: tauraro sifili alama lamba
Kayi nishadi a cikin shirin ka
Ka tuna cewa shirye-shiryen ka da suke da nishadi aciki kuma suka kunshi muhimman bayanai zasi amafanar da masu sauraronka sosai. Ka samu hanyoyin da zaka sa wakoki da labarai na gargajiya da na zamani a cikin shirin ka, zai janyo maka masu sauraro duka maza da mata.
Ka yada labaran nasarori
A kullum, mata manoma na shawo kan kalubale, kuma suna cin nasara a aikin su na noma. Ka nio wadan nan labaran nasarorin ka yada su a shirye-shiryen ka.
A ina kuma zan iya sanin yadda zan gamsar da mata manoma sosai a gidan radio
Adamou Mahamane, Fatouma Déla Sidi, and Alice Van der Elstraeten. 2014. Guidelines for the production of gender responsive radio broadcasts . Food and Agriculture Organization of the United Nations. http://www.fao.org/3/a-aq230e.pdf
Ma'anoni
Adalci Tsakanin Jinsi: Adalci Tsakanin Jinsi na nufin adalci tsakanin maza da mata a yayin da kake girmama babancin dake tsakanin su. Yana bukatar hanyoyi tsiraru domin cike gurbin dake tattare da rashin daidaito a yanzu da yasa mace ko namiji a matsayi na raun. A mislai: yin amfani da waya salula ta mata daban dan tabatar da cewa gidan radio ya yada ra’ayin mata sosai kamar yadda zai yada ra’ayin maza. Ko kuma canja lokacin hira ko damar koyarwa ta yadda zaiyi daidai da lokutan maza da mata.
Daidaita hakkin maza da mata: Daidaita hakkin maza da mata na nufin mata da maza na jin dadin hakki, da damomi da kuma dama a rayuwa ba tare da tauye musu hakkin ba ko kuma an musu wariya bisa banbancin jinsi. Daidaita hakkin maza da mata ya kunshi tabbatar da cewa fahimta, san rai, da kuma bukatun maza da mata an basu nauyin matsayi iri daya, kuma ya nuna a aikin, da nauyin aiki da hukunce-hukunce da mutane suke a rayuwa kuma suke aiki dasu-a misali: mata da maza suna da hakki daya a wurin daukan aiki, ko koyarwa, ko karin matsayi, ko kyakyawan yanayin wurin aiki da kuma albashi. Daidaita hakkin maza da mata na da tasiri sosai da kuma alaka da tsarin rayuwar mutane kamar: matsayi a cikin al’umma, shekaru, kabilanci da kuma karkatar da sha’awa maza ko mata, da yunkurin samun daidaito a wadan nan bangarorin.
Daukan Mataki akan Jinsi: Daukan Mataki akan Jinsi na nufin daukar mataki dan gyara rashin adalci a bisa banbanci jinsi ko wariya dan samun nasara daidaita hakkin maza da mata ko adalci a tsakanin jinsi. Yana nufin lura da kulawa da jinsi zai bada hanyar yadda zaa kir-kiri shirye-shirye, wanda bukatun maza da mata zaa shawo kansu, zaa kalubalanci wariya da zargi, sanan daidaita hakkin maza da mata zai yadu.
Godiya
Gudunmuwa daga: Doug Ward, da Karin bayanai daka Caroline Montpetit, Sylvie Harrison, da kuma Vijay Cuddeford
Wana aikin an dauki gudunar dashi ne daka gudunmuwar kudi da gwamnatin kasa Canada ta bayar ta hanyar ofishin ta na Harkokin Duniya na kasar Canada
This resource was translated with support from The Rockefeller Foundation through its YieldWise initiative.