Dauko kayan aikin Farm Rediyo na shirye-shiryen rediyo dan sauya su da daidai amfanin ka

Menene “dauko kayan shirye-shiryen rediyo da sauya su daidai amfanin ka”?

Akwai bayanai da labarai masu dimbun yawa kala-kala da zaka samu a rubuce, da yanar gizo, da gidan telebijin, da fina-finai da sauran abubuwan yada labarai. Wasu daka cikin bayanan da labararuka ana iya amfani dasu wurin kera shirye-shiryen rediyo masu muhimanci, da nishadantarwa da kuma fadakarwa.

Tun da aka kirkiro rediyo shekaru 100 da suka wuce, akwai shirye-shiryen rediyo ba adadi da aka dauko daka fina-finai, adabi, litatafan katun, shirye-shiryen telebejin, katun din jaridu, wasanin kwaikwayo, wasanin bidiyo da dai sauran su.

A wanan BH2 (Yadda masu shirye-shirye zasuyi), zamu bada karfin gwiwa wurin dauko bayanai daka rubuce-rubuce na takada da kuma na yanar gizo, tareda fakitin Mujalun Farm Rediyo (tattaunawa, wasan kwaikwaiyo, da kuma shimfidu) da labaran manoma na “Barza Waya”. Amma ka tuna cewa, da yawan kaidojin da ayukan da zamu tattauna anan na da tasiri akan duka ayukan da zaka iya daukowa ka sauya shi shirin rediyo.

Ta yaya dauko abubuwa daka wata kafa ka sauya su zuwa shirye-shriyen rediyo zasu taimakawa masu sauraro sosai?

Ta hanyar dauko abubuawa daka jaridu da suaran kafafen yada labarai, ka samu maudu’ai da yawa, kala-kala da zaka ilimantar tare da nishadantar da masu sauraronka.

Ta yaya zai taimakeni in samar da shirye-shirye masu inganci?

  • Ta hanyar samun cikakun bayanai da labarai.
  • Ta hanyar gabatar da bangarori daban-daban masu muhimanci a cikin alumma wadanda watakila ba a saba da su ba.
  • Ta hanyar nuna yadda wasu al'ummomi suka tunkari matsalolin da kuke fama dashi yanzu.
  • Ta hanyar bayar da shawarar hanyoyi daban-daban na gabatar da al’amura - misali, wasan kwaikwayo, tattaunawa tsakanin masu gabatarwa, muhawara, wakoki, da sauransu.

Ta yaya zan fara?

  1. Fassara
  2. Wuri, suna, da kuma al’ada
  3. Shawarwari dangane da daukowa daka saura kafofin yada labarai daban-daban
  4. Abubawan da ya kamata ayi da kar ayi wurin amfani da abubuwan da ake dasu a kasa
  5. Misalan dauko abubuwa daban-daban na FRI dan amfani dasu
    • Shimfidai
    • Wasanin kwaikwayo
    • Tattaunawa
    • Labaran Barza Waya

Cikakun Bayanai

1. Fassara

Wataƙila abu mafi mahimmanci kuma hanya da ta zama dole a wurin dauko abubuwa daka wata kafa a sauya zuwa rediyo shine fassara abin zuwa harshen yada shirye-shiryenku.

Domin tabbatar da fassara ka tayi daidai da masu sauraron ka da kuma gudun cenja muhimman abubawa daka ainihin na farkon, ga wata shawara: Ka samu mai fassara daya ya fassara abun daka ainihin yaren da aka wallafa zuwa harshen da zaka yada shiryen-shiryen. Sai ka samu wani mai-fassara ya fassara maka daka yaren da aka yada shirin zuwa shi ainihin yaren da aka wallafa shirin tun farko. Idan wanda aka sake fassarawa zuwa ainihin yaren yayi daban da ainihin shirin ta hanyoyi da yawa, toh akwai matsala.

Fassara mataki na farko ne kawai wurin daukowa da sauyawa. Zaka iya cenja bayanai, ko ka cenja salo, ko kuma ka cenja gundarin zancen dan ya zama mai gamsuwa a wurin masu sauraronka, sanan zaka iya cenja abubuwa da yawa. Ka sa a rai, idan zai yiyu, zaifi kyau ka dauko abu ka sauya a tsarin wadanan hanyoyin da farko —idan ka gama daidaita komai, sai ka fassara shi zuwa yaren da zaka yada labaran.

2. Wuri, suna da kuma al’adau

Wata hanya mafi sauki ta amfani da abun da ka dauko a wata kafa ka sauya shi dan shirye-shiryen rediyo shine canza wuri (ko wurare) da ayukan suka faru, da cenja sunayen mutanen da abin ya shafa. Ka tuna, duk da haka, dole ne ka sanar da masu sauraro cewa kayi cenja-cenje. Misali, kuna iya fadawa masu sauraren ka asalin kafar da aka dauko shi wanda aka yi a wuri kaza (sai ka fadi asalin wurin), kuma ya shafi mutanen da aka canza sunayen su don shirin ya zama mafi dacewa da inda kuke.

Shawara game da cenja sunaye da wurare:
• Idan ka zabi sabon suna don maye gurbin sunan mutum na asali, KADA ka yi amfani da sunan da yake sanan ne a yankinku. Akwai yiyuwar masu sauraron ku zasu iya dauka kuna magana ne akan wani da suka sani. A madadin haka, ku zaɓi sunan da ba a sani ba sosai.

3. Shawara wurin dauko abu daka wata kafar

Idan kuka zauna kuka rubuta wata tattaunawa da kukai a shirinku sannan kuma kuka kwatanta yadda yake a shafin rubutu tare da rubutun da ya kamata a karanta shi a zuciya, zaku ga cewa an tsara matanin guda biyu daban.

Abun da wanan yake nufi shine, idan zaka dauko abu da yake a rubuce ka sauya shi zuwa rediyo, ya zama wajibi kayi aiki tukuru wurin sauyawa. Dole ne a rubuta tattaunawa ta rediyo cikin salo na hira amaimakon salon da yawanci ake samu a shafukan rahotanni, da littattafai, da littattafan da ba na kage ba, ko jaridu.

Duk da haka, albarkatun FRI kamar rubutun tattaunawa, wasan kwaikwayo, da labaran Barza Waya an tsara su ne don su zama “masu sauki a shirin rediyo.” An rubuta su cikin yaren tattaunawa kuma galibi basa dauke da kalmomin shirme da masu bukatar bayani. Amma kodayake albarkatun FRI sun dace da rediyo, duk da haka kana buƙatar karantawa a hankali kuma kayi gyare-gyare a inda ya cancanta, musamman idan zaka yada shi a cikin wani yare daban da Turanci ko Faransanci da aka rubuta su tun asali.

4. Abubawan da ya kamata ayi da kar ayi wurin amfani da abubuwan da ake dasu a kasa

1. Kada ka gabatar da tattaunawa ta bogi

Idan kana son sauya wata tattaunawa da kake da ita, ko labarai, dole ne ka gaya wa masu sauraron ka game da kowane canje-canje da kayi. Kana iya yin ƙananan canje-canje, kamar canza sunaye da wurare. Amma idan ka gabatar da tattaunawar — da sunaye da wurare daban-daban fiye da hirar ta asali - kamar dai da gaske ne ta faru, toh wannan yaudara ce. Kana gabatar da tattaunawa ta bogi a matsayin ta gaske. Anan akwai wasu abubuwan da zaka iya yi amaimakon haka.

  • Yi amfani da sunaye da wurare na asali amma ka gabatar da hirar a matsayin wacce aka gudanar tare da ainihin wadanda aka tattauna dasu a asalin wurin a asalin kwanan wata, koda kuwa baka zama a cikin yankin-ko ma a cikin ƙasar.
  • Ka faɗa wa masu sauraron ka cewa ka kirkiri labarin ne daka wata hira ta asali ta hanyar canza suna (sunayen) da wuri (wuraren) a cikin tattaunawar da canza wasu bayanai don hirar ta zama mafi amfani da dacewa ga masu sauraron ka. Don haka, kana bada labarin hira da ka kirkiro, tattaunawa ta kwaikwayo, ko da yake ta dogara ne akan wata ainihin hira.

2. Wataƙila mafita mafi amfanin (duk da cewa yana ɗaukar lokaci da kudi) shine gudanar da tattaunawar ka akan abu ɗaya ko makamancin maudu’i tare da manoma da sauran mutanen yankinka. Kana iya amfani da hirar ta asali a matsayin abun dogaro.

A yayin dauko abun da sauyawa zuwa rediyo:

  • Kaduba dukkan “lambobin.” Yawancin rubutun FRI da labaran Barza Waya suna ɗauke da lambobi da yawa: bayani akan yawan buhun-huna ko kilogram na masara da aka girba, tarin girbin wake a wani yanki, yawan lokutan da manomi zai cire ciyawa ko amfani da magungunan ƙwari, da yawan kuɗin da suka karɓa akan ko wana kilogram da aka sayar. Kada kawai ka ari lambobi daga rubutun asali. Dole ne ka maye gurbin lambobi a cikin rubutun ka ko labarin ka da lambobi da zasu bada ma'ana a yankin masu saurarenka. Gargadi: Wannan na bukatar bincike!
  • Ka tabbatar da cewa duk abinda ke cikin rubutun ya dace da al'adun yankinka-misali, mata na iya zama ‘yan kasuwar masara a yankinku amma ba a yankin da aka sanya ainihin hirar ko wasan kwaikwayon ba. Don tabatar da cewa labarin ya dace da yankinka, ka canza waɗannan bayanan kafin yada shirye-shiryen.
  • Ka dauko bayanan noma ka sauya su da wanda aka fi sani a yankinka. Misali, zaka iya cenja:
    • Kwari da cututuka da aka fi samu a yankinka.
    • Kayan amfanin gona na yau da kullun da sauran albarkatun gona da ake dasu a yankinku.
    • Ayyukan noma wanda ya zama ruwan-dare (ko sabo) a yankinka da suka danganci shirya ƙasa, cire ciyayi, girbi, kula da kwari da cututtuka, adanawa, tallatawa, da sauransu. Wannan na iya buƙatar bincike.

5. Misalin dauko albarkatun FRI tare da sauya su dan amfani dasu

Dauko shimfida shirye-shirye da fakiti alamuran

Abubakar A. Kadir daka North Star FM a Tamale, kasar Ghana, ya dauki wadanan matakai na dauko shimfida akan tsutsotsin kaka na FRI tare da sauyawa dan amfani dasu.

  1. Ya dauko maudu’in tsutsotsin kaka wurin shirye-shiryen yau da gobe saboda babbar matsala ce a yankin masu sauraron sa.
  2. Ya karanta shimfida akan tsutsotsin kaka, a kafar yanar gizo. Ya raraba shimfidar zuwa sashe shida, a tsarin sa na watsa shirin tsutsotsin kaka sau biyu a wata har tsawon wata uku, sanan kuma ya tabatar da cewa ya watsa shirin daidai da kalandar aikin gona. Shashin shida sune:
    1. Banbanta rundunar tsutsotsi da sauran kwari.
    2. Hanyoyin kariya na maganin tsutsotsin.
    3. Amfani da magnin kwari. (Domin anyi amfani da magungunan kwari a gaba daya lokacin shuka, wanan maudu’in anyi bayanin sa a jerin shiryen-shiryen.)
    4. Almara da rashin fahimta game da tsutsotsin kaka.
    5. Shirin da aka wallafa akan mata manoma.
    6. Takaitacen bayani akan dukan batutuwan.
  3. Ya bada shifidar bayanan ga duka ma’aikatan shirin (mai gabartarwa, mai shiryawa, da kuma takanishiyans guda biyu) su karanta. Suka hadu suka zabi maudu’in da yafi dacewa daka shimfidar bayanan.
  4. Kadir (mai gabatarwa) da shugaban shirin suka fasara muhimman bayanan zuwa yaren Dagbani, sanan suka rubata tsarin shirye-shiryen da yaren Dagbani. Ko wana shirin, an raba shi zuwa kaso uku: 1) Gabatarwa da hirar pop; 2) Hira da babban bako; da kuma 3) shirin kiran waya.
  5. Tim din sun tuntubi manyan bakin nasu wanda suka dace da kowana shirin. Sun tura tambayoyin su da wuri sanan sun gudanar da tautaunawa ta gwaji da Ma’aikatar Abinci da aikin Gona a sati daya kafin watsa shirin.
  6. Tim din na zuwa fili suyi hirar da mutane kafin su watsa ko wana shirin.
  7. Tim din suna yin taron bayan fage don tattaunawa akan ko sun cimma burin su, sanan suga ko akwai abin da za'a iya ingantawa.

Abdul Dahim mai gabatarwa ne wanda yayi aiki a da tare da gidan rediyon Might FM amma yanzu yana aiki da Rediyo 123 a garin Tamale, kasar Ghana. Ya dauko fakitin alamuran da akeyi bayan an girbe wake na FRI ya sauya su zuwa amfanin sa.

  1. Dahim da ma’aikatan shirin (mai taya gabatarwa, da mai bada umarnin tashar, da kuma akawu) sun karanta fakitin kowanen su daban-daban.
  2. Bayan sun gama karantawa, Dahim da mai taya shi gabatarwa sun kirkiro tambayoyi dan su tambayi bakon nasu a lokacin da ake yada tattaunawa kai tsaye.
  3. Kwana biyu ko uku kafin a yada shirin, suna daukar wani bangaren na Shimfidar Bayanai dan su saka a cikin wasu bangarorin shirin. Misali lokacin da suke fita fili, sun hadu da wani manomi da yayi asarar amfanin gonar sa ta hanyar cutar funfuna dalilin kasar gonar sa babu ruwa sosai. Sun fara shirin ne da hirar da sukai da wanan manomin yana bada labarin sa. Shirin ya kunshi amfanin jakar PIC, cikakun bayanai da aka dauko daka fakitin alamuran wake.
  4. Tim din ya ajiye kwapi daya na fakitin al’amuran a situdiyo dan bada misali lokacin da ake yada shirin kai tsaye.

Gideon Sarkodie na gidan rediyon ADARS FM a garin Kintampo, kasar Ghana, ya dauko shimfidar bayanai akan masara ya sauya ta zuwa amfanin sa.

  1. Ya gudanar da tattaunawa da wasu rukunin mutane kadan a unguwanni da neman sanin ko alummar unguwannin sun gane maudu’in da ake magana akai. Ya kawo ‘shimfidar bayanai’ a rubuce a cikin wayar sa, sanan yayi amfani da ita wurin kirkiro tambayoyi ga manoma. Ya ba da hankali akan “Muhimman bayanai” a cikin ‘shimfidar bayanai’ sanan yayi tambayoyi kamar haka: Ya ka fahimci wanan muhimmin bayanin? Me ka fahimta da girbi da wuri, tantancewa, tarwatsawa, da kuma busarwa kamas, me kake ganin zai magance kwari, dss?
  2. Ya gano manoma sun damu su san lokacin da yafi dacewa suyi girbi, da busarwa da kuma adanawa. Ya lura da yawan mutane suna so su adana masara a dakunan da babu iska sosai, saboda ya tattauna akan yadda za’a samu wadatacen wurin ajiya ya kuma jadada fa’idar amfani da jakunkuna, mazubi da kuma jakunkunan PICS.
  3. Yayi amfani da muryoyin manoma a mtsayin hirar sa da manoma a shirin sa na manoma.

Dauko wasan kwaikwayo da sauyawa dan amfani dashi

Abdul Dahim daka Rediyo 123 a garin Tamale, kasar Ghana, ya dauko wasan kwaikwayo mai suna Abota da noma: Hada noman wake da hatsi ya sauya shi dan amfanin dashi.

Ma’aikatan shirin sun tuntubi rukunin masu wasan kwaikwayon yau da kullun sun roke su da su ƙirƙiri tattaunawar da ba a rubuta ba tsakanin 'yan wasa biyu-manoma, don wani ɓangare na shirin. Ma’aikatan shirin tuni sun karanta shimfidar bayanai ta wake kuma sun dau abun da zasu dauka sun rubuta da yaren Dagbani akan wana maudu’i zasu saka cikin tattaunawar (misali: Jakunkunan PICS, cutar funfuna), sanan sun roki yan wasa masu hawa kan murya su cusa wadanan maudi’en a cikin tattaunawar tasu.

Ga matakan da Dahim da ma’aikatan shirin suka bi wurin dauko wasan kwaikwayo da sauyawa:

  1. Bayan ya gama karanta tsarin-labaran, masu rukunin shirin, sunyi shawara akan wana bayani ya kamata a cenja-misali, cenja sunayen musulmi zuwa na kiristoci, tabatar da samuwa daidaiton jinsi, sunayen wurare, da kuma sauti (misali, idan sautin SGX yace ganga, masu shirin, sun zabi ganga ko waka da aka fi sani yankin dan dacewa da lamarin).
  2. Maus shirya shirin, sun lura da wana cenja-cenje kuma sun buga su a takada sun rarabawa yan wasa masu hawa kan murya.
  3. Masu shirya shirin sun rage tsayin gabatarwan wasan kwaikwayon (abun lura ga me gabatarwa) ta zabar muhimman abubuwa da suka rubuta da yaren Dagbani dan yan wasa masu hawa kan murya sun karanta. Labarin ya haifar da “tsokaci” da ya kasance tsawon dakika biyar kuma ya gabatar da haruffa da mahallin a cikin Dagbani. Dahim ya lura cewa doguwar gabatarwa a cikin turancin tayi amfani, domin ita ta jagorantar da samun gajeren labarin a yaren Dagbani.
  4. A maimakon fasara tsarin-labaran kalma da kalma, yan wasan masu hawa kan murya suna karanta tsarin-labarin ne tuni, suna nazari akan sa, suna kula da abubwan da suka dace suna rubutuwa. Wanan yay a taimaka musu wurin samar da nasu tsarin-labarin a yaren Dagbani da yafi sauki.
  5. Dahim da tawagarsa sun nadi dukkanin wasan kwaikwayon kai tsaye a cikin filin kuma sun dawo da shi situdiyo don gyara.

Gideon Sarkodie daga gidan rediyon ADARS FM, ya dauko wasan kwaikwayo mai suna http://scripts.farmradio.fm/radio-resource-packs/103-2/7-papa-akwesi-learns-careful-post-harvest-management-maximizes-maize-income/

Ya gano cewa wasan kwaikwayon ya yi tsayi da yawa a cikin shirin nasa, don haka ya yi amfani da wani ɓangare na wasan kwaikwayon kuma ya nemi manoma su ba da kansu don yin wasan kwaikwayo. Akwai yan wasa huɗu aciki kuma sun yi amfani da sunayen ainihin yan wasan. Gideon ne ya bada umarni, kuma ya fara yin gwajin wasan kwaikwayon ne har sau huɗu, sannan suka yi rikodin wasan kwaikwayo na minti 15 na ƙarshe. A lokacin rabin shirin na farko, bangaren shirin ya maida hankali kan aflatoxin ne ta hanyar karanta bangaren wasan kwaikwayo da yake magana game da aflatoxin.

Wasu abubuwan lura wurin dauko wasan kwaikwayo dan sauyawa ayi amfani dasu

• Wani mai gabatar da shirye-shirye a kasar Ghana ya tsara wasan kwaikwayo game da amfani da takin gargajiya ta hanyar yada wata muhawara inda mutum daya ya bada fa'idar amfani da takin gargajiya wani kuma yayi magana game da kalubalen amfani da takin gargajiya kuma ya kawo hujojji alkairin dake dauke da amfani da takin zamani.

• Regina Suwie ta gidan rediyon Progress a garin Wa, kasar Ghana, ta tsakuro baitocin wakoki daga tsarin-labarin wasan kwaikwayo na wake.

• Selorm Deyegbe daka gidan rediyon Jubilee a garin Keta, kasar Ghana, yayi amfani da bayanan da ya samo a wasan kwaikwayon akan kududifin kifi a matsayin shimfidan shirin sa, saboda bai samu yan wasan kwaikwayo ba.

• Wani namiji mai gabatar da shirye-shirye a arewacin kasar Ghana na da rukunin yan wasan kwaikwayo wanda tashar ke haɗin gwiwa dasu. Mai gabatarwa yana bawa yan wasan kwaikwayon tsarin-rubutun sai su gyara rubutun suje su zaɓi yan wasa kuma su shirya wasan kwaikwayo. Sannan suna gwaji akan tsarin- rubutun wasan da ƙungiyar ta gyara don aiki a matsayin wasan kwaikwayo. Kungiyar tana kawo tsarin-rubutun wasa wurin gwajin don tabbatar da cewa babu wani abu mai mahimmanci da ya ɓata a cikin tsarin-rubutun wasan, kuma masu gabatar da shirye-shiryen suna yin gyare-gyare kan rubutun, akwai wasan gwaji guda biyu da akeyi don tabbatar da cewa tsarin-rubutun wasan yayi daidai da yadawa, sannan kuma sai a yi rikodin.

• Wata mace mai gabatar da shirye-shirye, daka arewacin kasar Ghana, tace ita tashar ta na amfani da wani rukunin masu wasan kwaikwayo da suke kira duk sanda FRI suka turo musu wasan kwaikwayo. Suna haduwa da rukunin su karanta wasan kwaikwayon. Idan an gama fasara wasan kwaikwayon zuwa yaren Dagbani, rukunin sai suyi wasan gwaji. Wani sa’in, masu shirin gidan rediyo suna karawa ko cire wasu abubuwa daka cikin wasan kwaikwayon—“Akwai wasu kalmomin da baza ka iya fassara su zuwa Dagbani ba.” Sai suyi rikodin wasan kwaikwayon.

Adam Hussein daka gidan rediyon Might FM a garin Tamale, kasar Ghana, yace tashar su na da hanyoyi biyu na yin wasan kwaikwayo, a cikin sitidiyo da rukunin masu kwaikwayo, da kuma a waje ta hanyar amfani da manoma da wasu mutanen gari.

A cikin situdiyo:

  • Adam na buga tsarin rubutun wasa ne a takada ya bawa mai bada umarnin wasan. Su biyu sai su zauna su tattauna akan wasan, suyi gyara a inda ya dace (yawanci sunaye ne kawai da wurare), sai mai bada umarnin ya zabi yan wasa da rawa da kowa zai taka.
  • Rukunin sai suyi gwajin wasan.
  • Bayan anyi gwaji sosai, sai su dawo cikin sitidiyo suyi rikodin wasan. Sautin ana samo shine in an fita filin aiki (ba’a yanar gizo ba). Ba daya daka cikin yan wasan da yake da tsarin-rubutun wasan a hanunsa; suna hadda cewa ne ko kuma suna bin umarnin mai bada umarni.

In an fita filin aiki:

  • Adam na nada manomi guda jagora ya kuma bada umarni. Kamar yadda akeyi a sitidiyo, shi da wanda ya nada jagora suna tattaunawa akan tsarin-rubutun wasan, sai su gayawa kowa rawa da zai taka, sanan su fara da gwajin wasan.
  • Yan wasan masu hawa kan murya a filin aiki basu da kwafi na tsarin-rubutun wasan. Sai dai kawai, mai bada umarni ya karanto musu abun da za suce sai su maimaita. Wanan yana taimakwa a inda yan wasan basu iya karatu ba. Adam ne ke rikodin muryoyin su.
  • Haka zalika Adam ne ke rikodin duka sautin a filin aiki.
  • Adam yana kawo duka rikodin din gidan rediyo sanan shi da mai kula da tashar sai suyi gyare-gyaren rikodin din. Tsarin tattarawa da shirya shirin yana daukar kusan kwana uku. Sanan sai a yada wasan kwaikwayon.

Dauko tsarin rubutun tattaunawa da sauya shi dan amfani

Eric Wilson mai gabatar da shirye-shirye ne a gidan rediyon Word FM a garin Bolgatanga, dake kasar Ghana. Ya lura cewa rukunin masu tsara shirye-shirye na cusa tsarin-rubutun tattaunawa na FRI a kowana shirin su a duk inda suka samu dama kuma ya dace.

Ya dauko wata hira mai suna Adana gona: Yawan albarka, karancin kudin noma, da kuma samun ingantaciyar kasar shuka.

Wadanan mataken ne shida rukunin masu shirya shirin suka bi:

  1. Daka tsarin-rubutun, mai shiryawa ya samo masanin da za’ai hira dashi.
  2. Mai shiryawar ya bawa masanin takardar tsarin-rubutun.
  3. Mai shiryawar ya fasara tsarin-rubutun zuwa yaren yankin—ba wai fasara kalma da kalma yayi ba, kawai ya rubuta abun da ya lura na da muhimanci da yaren garin ya buga a takada. Sai mai shiryawa da masanin sukai aiki da tsarin-rubutun a wurin hirar da suka yada, suka ajiye kwafi daya na tsarin-rubutun dan misali a lokacin yada shirin.
  4. Bangare na biyu na hirar tattaunawa ce da manomi. Mai shiryawar yayi tattaki zuwa gona dan tattaunawa da manomi. Yayi rikodin tattaunawa ta amfani da tambayoyi iri daya da suke cikin tsarin-rubutun tattaunawa, ya cenja sunayen mutane ne kawai da wurare.

Earl Samuels shine mai gabatar da shirin safe da shirin manoma a gidan rediyon Suhupielli FM a garin Tamale, kasar Ghana, kuma yana amfani da tsarin-rubutun tattaunawa akai-akai. Yana farawa ne ta hanyar karanta mujallah da kuma tattauna manyan batutuwan tare da tawagarsa ta masu koyo guda takwas (wanda ya hada da masu gabatarwa, masu shiryawa, da editocin labarai daga gidajen rediyo daban-daban).

Mista Samuels wani lokacin na amfani da tsarin-rubutun tattaunawa hade da mujalun ‘shimfidar bayanai’. Misali, a wani shirin da yayi kwananan akan kasar shuka, ga dabarun da yayi amfani dasu:

  1. Ya karanta tsarin-rubutun tattaunawa (Adana gona: Yawan albarka, karancin kudin noma, da kuma samun ingantaciyar kasar shuka).
  2. Ya ziyarci manoma ya tambaye su akan kalubalen da suke samu akan kasa.
  3. Ya turawa wani masani tsarin-rubutun wanda ya shahara a bangaren. Tare, sai suka fitar da abubuwa masu muhimanci da zasu tattauna akai a cikin shirin, akan abun da Mister Samuel ya koya a filin aiki.
  4. Mister Samuel ya hada wasu bayanai da ya samo a mujalun ‘shimfidar bayanai’ masu suna Amfani da rufafiyar kasa ta dun-dun dan adana gona da ya fadada wasu tambayoyin a tsarin-rubutun tattaunawa.
  5. Tsarin-rubutun an fasara shi zuwa yaren garin.
  6. Mister Samuels ya karanta bangaren tattanawa a lokacin da ake yada hira da masanin. Shi da masanin basu tattauna tambayoyi da amsoshin a yanda suka zo a ainihin tsarin-rubutun kalma da kalma ba; a maiakon haka, sai sukayi hira a matsayin kansu suke wa tambayoyi suke bawa kansu amsa. Tsarin-rubutun ya samar musu da tambayoyin tattaunawa, amma Mister Samuel ya kara dogara dasu wurin yadda tambayoyin zasu zo daya bayan daya. Mister Samuel da masanin dukan su na dauke da tsarin-rubutun a takada a hanun su a lokacin da ake yada shirin. An fasara komai zuwa yaren yan garin.

Gideon Sarkodie daka gidan rediyon ADARS FM a garin Kintampo, kasar Ghana, ya dauko tsarin-rubutun tattaunawa na Gwara a siyar gaba daya tare: Amfanin hada kai ayi talla a tare ya sauya shi dan amfanin sa.

1. Ya samu tsarin-rubutun ne cikin wayarsa a yayin da yakai ziyara filin aiki tare da mai taya shi gabatarwa, anan suka hadu da manoma dan tattaunawa akan amfanin hada kai a siyar tare. Sunyi amfanin da tsarin-rubutun tattaunawa a matsayin wani madubi akan tallata kaya tare. Sun lura sun iya amfani dashi wurin tattaunawa akan masara a kasar Ghana, duk da cewa ainihin rubutun yana Magana akan rogo a kasar Tanzania.

2. Wasu tambayoyin da sukai wa kungiyar manoma sun dauke sune kai tsaye daka cikin tsarin-rubutun, kuma sun gwada amsoshin su da abun dake cikin tsarin-rubutun.

A wasu lokutan, Gideon da mai tayashi gudanar da shirin, kawai suna karanta bangaren manomin da mai masa tambayoyi a cikin shirin, suna fasarawa zuwa yaren yan garin, Twi, a yayin da dukan su na dauke da bugun tsarin-rubutun a takada a hanun su a lokacin da ake yada shirin. Suna cenja sunaye, tsarin wurin, da sunayen wurare, dan ya zama daidai da yanayin kasar Ghana.

Dauko labaran Barza Waya da sauya su

Abubakar A. Kadir daka gidan rediyon North Star FM a garin Tamale, kasar Ghana, yayi amfani da wadanan matakai wurin dauko DRC: Manoma sun gwada hanyoyi uku wurin kula da tsutsotsin kaka dan yayi amfani dashi.

  1. Yana karanta labarin sanan ya ziyarci shafin yanar gizo na FRI dan neman karin bayani.
  2. Labarin yayi magana akan bibiyar gona dan neman tsutsotsin kaka da lalacewar shuka. Wanan ya tunawa Kadir da lokacin da aka fara samun tsutsotsin kaka a kasar Ghana a shekara ta 2016. Ma’aikatar abinci da gona sun raraba bayanai ta yadda zaka gane kwarin da kona shukar, amma wanan bai wadatar ba.
  3. Kadir yayi maganar a lokacin da ake yada shirin, sanan ya tattauna akan hanyoyi uku da akai amfanin dasu, tare da jadada sa ido akan gona da kuma kona shukokin da suka kamu da cutar saboda hanya ce mai kyau a gonakin da basu kamu da cutar gaba daya ba.

Earl Samuels na gidan rediyon Suhupielli FM shima na amfani da labaran Barza Waya. Yana yawan amfani da labaran wasu kasashe. Yana karanta labaran ne a lokacin shirin sa, yana fadar cewa daka wata kasar ne, sanan ya bada shawara manoma su dauki dabarun dake cikin labarin. A shirye-shiryen nashi na gaba, yana tambayar manoma ko hanyar da suka dauka tai musu amfani ko suna bukatar yan gyare-gyare, sanan yaji ko akwai bukatar sake fadin bayanan.

Gideon Sarkodie na rediyon ADARS FM na karanta labaran Manoma na Barza Waya a shirin sa. Yana fasara ainihin gundarin aikin zuwa yaren Twi, sai yayi bayani cewa yana karanta labarin Barza Waya ne na Farm Rediyo daka wata kasar, sai yayi wa masu sauraron sa tambaya ko akwai wani ilimin gargajiya a Ghana da za’a iya amfani dashi.

Edwin Mpokaye shine mai kula da tashar Radiyo Fadhila FM a yankin Mtwara dake kasar Tanzania. Yana yawan amfani da labaran Barza Waya a lokacin da yake watsa shirye-shiryen sa, mai sunan Dandalin Manoma. Ya dauko labarin Barza Waya na Malawi: Manoma na hada fitsari da takin ganye dan su rage kashe kudi ya sauya shi dan amfani wurin shirin sa. Yana fasara labarin zuwa yaren Swahili sanan ya karanta a lokacin da yake w yada shirin sa. Ya gabatar da maudu’in da ainihin wurin a farkon bada labarin. Alhalin ya bar bayanai da yawa dake cikin ainihin labarin, ya cire wasu lambobi da basu da amfani a wurin manoman dake yankin sa, kamar kudin takin zamani a kasar Malawi. A karshen labarin, ya sanar da cewa daka Farm Rediyo International, kasar Kanada ya dauko.

Sources of information

Wanda ya gudanar da attaunawa da masu gabatarwa a arewacin kasar Ghana shine Maxine Betteridge-Moes, mai taimakon sa kai Uniterra, na Farm Radio International
Taron karawa juna sani na jin ta bakin masu gabatarwa, wanda akai a garin Tamale, a watan Maris 2017, wanda Vijay Cuddeford ya shirya, Manajin Edita, na Farm Radio International.

Acknowledgements

Gudunmuwa daka: Vijay Cuddeford, Manajin edita, Farm Radio International.


Wanan aikin an fasara shi daga tallafin da Ma’aikatar Tarayya ta Hadin Gwiwa Tattalin arziki da Cigaba ta kasar Jamus ta cikin Deutsche Gesellschaft für Internationale Zusammenarbeit GmbH (GIZ) da kuma abokiya hulda ta “Green Innovation Center for the Agriculture and Food Sector” a Nijeriya.