Tattaunawa da Kwararru: Nagartattun ayyuka domin masu gabatarwa da kwararru
Gabatarwa
Tattaunawa da kwararru kan taimaka sosai ga shirinka na radiyo akan manoma. Ta kan bawa masu sauraronka bayanan da za su dogara da su daga tushe na gaskiya. Kuma kada ku manta – wasu daga cikin manoman su ma kwararru ne.
A lura da cewa wannan bayanin na “Jagoran mai gabatarwa” an yi shi ne don masu gabatarwa da kwararru, saboda yana da mahimmanci ga rukunan biyu su san ayyuka da dabi’un da suka dace na mutanen da suka halarci tattaunawa.
Ta yaya tattaunawa da kwararru za ta taimaka min na gamsar da masu sauraro na?
- Za ta tabbatar da cewa masu saurarona sun samu sabbin bayanai da suke bukata.
- Za ta karfafa ilimi da kwarewar masu sauraro da basu damar bincike da kuma sanin gundarin bayanai, ko kuma don su san ilimin al’ada wanda ke da daraja.
- Za ta karawa masu sauraro kwarin guiwar cewa suna amfani da hanyoyin noma masu tasiri, ko ta taimaka musu su sauya wasu haanyoyin noman da basu da tasiri.
- Za ta taimakawa masu sauraro wajen samun sabon ilimi da kuma fahimtar sabbin hanyoyi.
- Za ta bawa masu sauraro kwarin guiwar yin magana da malaman gona da sauran kwararru a garuruwansu.
Ta yaya za ta taimaka min na samar da shirye-shirye masu inganci?
- Za ta kawo hadin guiwa tsakanin ma’aaikan radiyo da kwararru.
- Za ta tabbatar da shigowar kwararru a dama da su a cikin shirina na radio.
Ta yaya zan fara?
- Ka shirya sosai
- Farko da karshe
- Ka zama mai girmama mutane
- Ka yi amfani da dabarun tattaunawa masu kyau
- Akwai wani banbanci tsakanin tattaunawa da kwararrun masana kimiyya da kuma tattaunawa da kwararrun manoma?
- Sabanin ra'ayi, da banbancin fahimta a kan ilimi
- Magance matsaloli
- Kawar da al'adu marasa kyau da kuma sauran abubuwan da suke hana tattaunawa ta yi kyau
- Maza su tattauna da mata sannan ata su tattauna da maza
- Ka kulla alaka
Cikakkun bayanai
1. Ka shirya
Don mai gabatar da tattaunawa:
- Ka yanke shawara a kan maudu’i da fagen tattaunawa. Ga misali:
- "A yau, za mu tattauna a kan ciyar da kaji kwari. Za mu yi bayanin kwari daban daban da ake amfani da su, Hanyoyin da suka fi sauki wajen kamo su da kuma kiwonsu, da amfani da kuma kalubalensu ga manoma."
- Ka shirya taattaunawar sosai tun kafin lokacin don tabbatar da cewa kwararen da aka gayyata yana nan, kuma ka sanar da shi tsawon lokacin da tattaunawar za ta dauka.
- Ka yi dan bincike a kan maudu’in, don ya kasance cewa ka fahimci batutuwa da tambayoyi masu mahimmanci. Idan za kai tattaunawa da malamin gona, yi kokari ka ji ta bakin wasu manoman kafin nan, don ya kasance ka na da tambayoyin da za ka yiwa kwararru da ka san manoma na bukatar amsarsu.
- Ka yi dan bincike game da kwararren da za ka tattauna da shi, da kuma fagen da ya kware. Ka shirya tambayoyinka sosai domin su jagoranci wanda ake tattaunawar da shi ya mayar da hankali a kan maudu’in da ake tattaunawa a kai. Idan ba haka ba, sai ya kasance kwararren ya mamaye taattaunawar da wasu maganganun da kuma mayar da hankali a bangarorin da ba lallai ne suna da alaka da maudu’in ba.
- Ka tabbata cewa tun kafin tattaunawar wanda za a tattauna da shi ya san cewa za a nadi tattaunawar, kuma za a iya yadata.
- Ka tabbata cewa kwararren ya san su waye masu sauraron: Ga misali, Kananan manoman rogo wadanda basu shafe shekaru da dama a makaranta ba, kuma za su fi fahimtar sakon magana da bashi da tsauri.
- Ya dace mai gabatarwa ya aikawa kwararre jerin tambayoyin da za a tattauna? Duk da cewa mutane da dama na ganin ya dace su yi hakan, akwai wasu matsaloli da ke tattare da yin hakan. Bayar da jerin tambayoyin kafin tattaunawar ka iya sanya kwararren ya dinga jan akalar tattaunawar da kuma fadar wacce tambaya za a tambaya – da kuma amsa. Haka kuma, a maimakon ya amsa tambaya daya a lokaci guda (wadda zai gina a kan ilimin da masu sauraro ke da shi yanayi na mataki-mataki), Kwararre ka iya amsa tambaya daya, sannan yayi ta jawabi wanda ya kunshi amsoshin wasu tambayoyin, amma babu wani cikakken bayani, kuma babu damar bibiya. Saboda wadannan matsaloli, shi yasa zai fi kyau mai gabatarwa ya sanar da kwararre tun kafin tattaunawa (Ga misali, lokacin da ake shirya tattaunawar ta wayar tarho) game da maudu’in da za a tattauna a kai, da kuma jerin irin tambayoyin da kwararren ka iya tsammani. Ya kamata wannan shiri na tattaunawa ya kunshi cikakkun bayanan da suka dace domin bawa kwararre damar shiryawa a kan maudu’in da za a tattauna a kai, amma ba tare da an bashi hakikanin tambayoyin da za a tambaya ba.
Domin kwararre:
- Ka yi nazarin maudu’in da za a tattauna, domin samun bayanan da suka dace, da kuma kwarin guiwa.
- Ka kashe wayarka kafin tattaunawa ta gaba-da-gaba domin rage raba-hankali biyu.
- Za ka iya rubuta taka fahimtar a kan wasu mahimman batutuwan a takaice kuma a saukake domin kaucewa rikicewa a yayin tattaunawa. Sai dai, ba zai yi kyau a radiyo ka dinga karanto amsoshinka kamar kana karanto rubutaccen darasi na makaranta ba. Ya kamata tattaunawa ta zamo tattaunawa tsakaninku, don haka ka amsa tambayar mai tambaya kamar yadda ya tambayeka, kuma a yanayi na tattaunawa.
- Ga misali, a kasar Uganda, kwararre kan iya shirya tattaunawa, ta hanyar rubuta jerin manyan camfe-camfe a kan jinsi da ke da alaka da ayaba: 1) Bai kamata matar aure ta je yanko ayaba ba saboda za a dinga kallonta a matsayin barauniya; 2) Mata ba za su sayar da ayabar da ake samar da lemo da ita ba; 3) Mata ba za su mallaki gonar ayaba ba.
A lura: A koda yaushe hakkin mai gabatarwa ne ya zabo maudu’in da za a tattauna kuma ya ja ragamar tattaunawar, saboda shi ne ko ita ce ya/ta san manufar shirin kuma yake da alhakin samarwa da masu sauraro bayanan da suke bukata.
2. Farko da karshe
Don mai gabatar da tattaunawa:
Farko:
- Idan ka taba tattaunawa da kwararren a baya, ka tunatar da shi game da tattaunawar da kuka yi a baya. Ka fada masa irin amfanawar da ta yi, sannan kuma, idan ba ka riga ka yi wannan ba, ka fada musu sakon da masu sauraro suka aiko da shi.
- Kafin ka yi magana, ka yi murmushi ga wanda zaka tattauna da shi, domin kulla alaka sannan ka gabatar da su yadda ya kamata.
- A lokacin daukar shiri da lokacin gudanar da tattaunawa kai tsaye, ka yiwa wanda za a tattauna da shi gabatarwa mai kyau. Misali, ka zayyano matsalolin da kake so ka tambayi kwararre game da su, da kuma tasiri da abubuwan da wannan matsala ke haifarwa. Sannan ka gabatar da wanda za ka tattauna da shi da kuma alakarsu da kwarewarsu a kan matsalar, ka kuma yi bayanin cewa kana bukatar karin bayani daga wajen kwararre. Ga misali,
- Sauyin yana yi na ci gaba da bawa manoma matsala, musamman a bangarorin da suke da bushewar kasa a nahiyarmu. Wadanne hanyoyi ne manoma za su dinga amfani da su bisa la’akari da sauyin yanayi? Muna tare da Mr. John Phiri, wani kwararre a fannin tasirin sauyin yanayi a kan samar da amfanin gona. Mr. Phiri zai taimaka wajen warware mana wadannan hanyoyi.
Karshe:
- Ka tunatar da masu sauraro taken tattaunawar da kuma bayyana musu wasu daga cikin bayanan da tattaunawar ta tabo a takaice. Ga misali, za ka iya cewa:
- "Kun saurari Patience Abdulai daga garin Tumu wadda ta yi mana bayanin abubuwan da ta sani game da noma mai cike da kariya. Ta bayyana cewa manyan abubuwan uku da ta amfana da su sune, saboda kasancewar tana da juna biyu kuma tana bukatar hutu sosai, noma dan kadan ne zai fi sauki. Haka kuma, sauya shuke-shuke ya bawa iyalanta damar samun kayan amfanin gona daban-daban, wanda ya taimaka musu a kasuwa da kuma samar da abinci. Kuma daga karshe, bayan ta yi noma mai cike da kariya na ‘yan shekaru, sai ta fara fahimtar cewa kasa mai kyau na samar da amfani mai kyau, kuma duk da cewa an dauki wasu ‘yan shekaru, yanzu ana samun ci gaba.” KADA kawai ka ce: kun saurari Patience Abdulai daga garin Tumu wadda ta yi mana bayani game da amfanin noma mai cike da kariya."
- Za kuma ka iya bukatar wanda ake tattaunawa da shi ya yi bayanin mahimman abubuwan da ka tabo a takaice.
- Ka bayyana godiya. Ga misali:
- Muna maka godiya kwarai da gaske da ka samu damar taattaunawa da mu a yau kuma muna fatan sake kasancewa da kai nan gaba a cikin shirin." Ko kuma a saukake: "Muna godiya da ka samu damar kasancewa a cikin wannan shiri a yau."
- Ka tabbata ka adana shirin da ka dauka, kuma ka adana shi da sunan da zai nuna maka wanda ka tattauna da shi karara, da kwanan wata, da kuma batun da aka tattauna.
3. Ka zama mai girmama mutane
Domin mai gabatar da tattaunawa da kuma kwararre:
- Ka guji fasa tattauna gab da lokacin da za a yi. Ka girmama cewa shi ma yana da abubuwan da ke gabansa. Kuma Idan dai ya zama dole sai ka fasa tattaaunawar to ka sanar a kan lokacin da ya dace.
- Ka kaucewa katse abokin tattaunawa akai-akai.
- Ka zo a kan lokaci!
- Ka saurari abokin tattaunawarka sosai.
- Ka kaucewa nuna yanayin gajiya, ko damuwa ko kuma fushi a fuskarka ko a jikinka. Ka kaucewa girgiza kai idan baka yarda da abinda abokin tattaunawarka ya fada ba.
- Ka kaucewa karyata abinda abokin tattaunawarka ya bayyana, Misali, "A’a, Manoma suna samun iri. Kawai dai malalata ne ba zasu je su samo ba." KO "Kwararru basa mayar da hankali a kan bukatar manoma, don haka na tabbata babu abinda hukuma za ta yi a kan wannan lamarin."
- Ka kaucewa jayayya ta yadda kowanne bangare zai ji cewa a kan daidai yake kuma yayi kokarin tabbatar da cewa dayan bai iya ba ko bashi da ilimi a kan abinda ake magana.
Domin mai gabatar da tattaunawa
- Ka karkare taattaunawar a karshen lokacin da aka shirya. Idan kana bukatar ka kara samun wasu bayanan, ka tambayi wanda ake tattaunawar da shi ko zai iya kara lokaci. Idan bai yarda ba, ka bukaci ya dawo wani lokacin.
- Ka kaucewa tambayar abin da ya shafi mutum ko tambayar da bata da alaka da abinda ake magana.
- Ka kaucewa fadar sunan wanda ake tattaunawa da shi ba daidai ba. Idan baka da tabbacin yadda ake fada, ka tambayi wanda ake tattaunawar da shi ya fada maka sunansa yadda yake kafin a fara tattaunawar.
- Ka sanar da wanda ake tattaunawa da shi lokacin da za a yada tattaunawar, a matsayin karramawa.
Domin kwararre:
- Kada ka daga waya ko ka dinga wasa da wayarka, ko karatu. Zai fi kyau ka kashe wayarka ko kuma ka kashe muryar wayar taka.
- Ka kaucewa bada gajerun amsoshi, wanda hakan yana alamta cewa kana so a yi maza-maza a kammala tattaunawar.
- Kada ka manta cewa mai gabatarwa ne ke da alhakin rike na’urar daukar shirin, ba wanda ake tattaunawa da shi ba.
- Ka kaucewa nuna cewa wanda yake tambayar bashi da ilimi.
- Kada ka mamaye lokacin shirin. Shirin na tattaunawa ne, ba darasi ba.
- Ka amsa tambaya daya a lokaci guda. Idan ka kawo wani bayani da mai tambaya bai tambaya ba, za ka iya bata tattaunawar gaba daya.
- Ka nuna godiya ga yadda mai gabatarwa ke isar da bayanai ga masu sauraro, kuma ka nuna ra’ayinka a kan yada ilimin noma ta kafafen yada labarai.
- Yana daga cikin aikin mai gabatarwa shi ne ya yi tambayoyin tabbatarwa da bin diddigi. A maimakon ka nuna baka son tambayoyin, ka yi maraba da su.
- Ka kaucewa girman kai da kuma nuna cewa "na san komai."
- Ka kaucewa sauya ra’ayinka game da abinda tattaunawar ta kunsa da kuma bukatar abubuwan da ba za a yi amfani da su ba.
- Ka kaucewa tunatar da mai yin tambaya game da kwarewarka a kai a kai.
- Ka kaucewa ci gaba da maimaita tambayoyin mai tambaya. Ga misali, mai tambaya ka iya tambayar cewa, "wanne nau’in ciyawa ne ke damun masara?" ka kaucewa maimaita taambayar kamar, ga misali, "wato idan muna magana a kan tsirrai marasa amfani da ke kawowa masara cikas, kafin shuka ta fito da kuma bayan shuka ta fito, wadanne manyan nau’ika?"
4. Amfani da dabarun tattaunawa
Domin mai gabatar da tattaunawa da kuma kwararre:
- Ka tabbata cewa tambayoyin da amsoshin sun ta’allaka a kan maudu’in.
- Ka dauki tattaunawar radiyo kamar tattaunawa tsakanin mutum da mutum. Ka zama mai girmama mutane da sakin fuska, Amma ka yi magana bisa ka’ida sama da yadda za ka yi magana da abokinka.
- Tsayin tattaunawa: gwargwadon tsawon tattaunawa ya dogara ne da makasudin tattaunawar da kuma yanayin shirin. A shirin da ya kunshi abubuwa da dama, tattaunawar da aka tace sai ta dace da sauran abubuwan da shirin ya kunsa, ka sa a ranka cewa tattaunawa ta mintuna 15 a kan maudu’i guda daya tare da mai binciken al’amuran noma ko malamin gona ka iya kunsar bayanai da dama manomi mai sauraro ba zai iya saurara a lokaci daya ba. A maimakon haka, za ta iya kasancewa bayanan mintuna 3 zuwa 5 sun wadatar. Kasashe daban-daban ka iya banbanta a kan aabinda suka dauka a matsayin tattaunawa da ake bukata, amma ka sa a ranka cewa babban makasudin shi ne samar da bayani mai amfani da manomi zai iya tunawa. Kafin tattaunawar, ka fadawa wanda za ka tattauna da shi cewa tattaunawar za ta dauki tsawon mintuna kaza, kuma sannan ka yi kokari ka dauki tattaunawar ta tsawon wadannan mintunan domin kaucewa gyrae-gyare da yawa.
- Domin shirin radiyo mai inganci, ya kamata kwararre ya yi magana ta ‘yan mintuna a lokaci guda, ba tare da mai gabatarwa ya yi wata tambaya ko ya katse shi da wata magana ba. Hakkin mai tambaya ne ya katse taattaunawa a kai a kai domin neman karin haske, ko kara wasu abubuwan, ko daidaita saurin tattaunawar, da kuma tabbatar da cewa mai tambayar da kuma masu sauraro duk sun fahimta.
Domin mai gabatar da tattaunawa:
- Ka bukaci kwararre ya yi bayanin batutuwan cikin sassaukan harshe, ba tare da wani shirme ba. Ka sa a ranka cewa ba kalmomi masu tsauri ne kadai ke zama shirme ba. Dukkan wata magana da bata cikin maganganun masu sauraro na yau da kullum shirme ce. ga misali, idan mai gabatarwa yana magana ne da harshensa na gida amma sai ya shigar da kalmomin aikin gona ko na lafiya da haarshen Turanci ko Faransanci, wannan zai zamo shirme a wajen masu sauraro. A koda yaushe ka yi kokarin nemo kalmar da ta dace ka yi aamfani da ita a harshenka na gida.
- Ka bawa kwararre isashen lokacin yin bayani.
- Ka kaucewa angiza kwararre domin ya dauki bangare a kan batutuwa, musamman idan akwai banbanci mai karfi tsakanin yadda ake kallon batutuwa masu mahimmanci.
Domin kwararre:
5. Akwai wani banbanci tsakanin tattaunawa da kwararrun masana kimiyya da kuma tattaunawa da kwararrun manoma?
- Akwai camfin da ake cewa wai kwararrun masana kimiyya sun san yadda za su yi tattaunawa mai amfani da tasiri. Gaskiyar lamarin shi ne wasu kwararrun suna da dabarun tattaunawa, wasu kuma basu da su. Wadanda ba su da su – da kuma wadanda kawai ba su da gogewa a bangaren tattaunawa – za su bukaci jagorancin mai tattaunawa da su domin ya taaimaka a samu tattaaunawar da za ta amfani masu sauraro. Ga misali, kwararrun masana kimiyya da ake tattaaunawa da su ba lallai su fahimci cewa wanda yake tattaunawa da su ne ke jan ragamar tattaunawar ba kuma za su so su ja akalar tattaunawar da kansu. Ko kuma ba za su ji dadi a katse su ba domin neman karin haske. Yi kokari ka yi musu takaitaccen bayani kafin fara tattaunawar a kan abinda za su yi tsammani, musamman idan baasu saba da taattaaunawa ba.
- Duka duka dai, ra’ayin kwararrun masana kimiyya ya fi karkata ne a kan bincike, yayin da ra’ayin manoma ya ke fitowa daga ilimi na yau da kullum da gogewa da kuma ilimi na al’ada.
- Tattaunawa da kwararrun manona sun fi shafar labarun kalubale, da fadi-tashi, da kuma nasarori, yayin da tattaunawa da kwararu ya fi shafar dunkulallun bayanai.
- "Babban banbancin shi ne game da fahimta. Fahimtar manomi ta dogara ne a kan gogewarsa a karan kansa, yayin da ita kuma fahiimtar kwararre ta dogara a kan rubutattun bayanai da nazari."
- Kwararren masanain kimiyya na kafa hujja da bincike da muka bayanan da aka yarda da su kuma kwararru suka tantance, kuma ake tsammanin zai kasance na gaskiya. Kwararren manomi na bada ilimi bisa gogewar da ya samu a karan kansa a muhallin da suke ciki, kuma ana tsammanin cewa akwai ra’ayi a ciki.
6. Sabanin ra'ayi, da banbancin fahimta a kan ilimi
- A yayin tattaunawa da kwararru, ka sa a ranka cewa daidaikun kwararru ka iya kasancewa da wani ra’ayi da ya saba da jin dadin manoma. Ga misali, zai iya kasancewa kwararre yana aiki da kamfanin samar da iri, kuma yana so ya tallata kamfanin a yayin tattaunawar. A irin wannan yanayin, yana da mahimmanci ga wanda yake tattaunawar da shi ya sanar da cewa kwararren yana aiki da wani kamfani da yake so ya jawo ra’ayin manoma domin su yi amfani da iri nau’i kaza.
- Haka kuma, kwararru – walau malaman gona, ko masu bincike, ko manoma – ka iya kasancewa masu ilimi sosai, amma su kullum basa kuskure; koda yaushe a kan daidai suke. Kuma a kan wasu batutuwan za ka samu cewa ba daya ba ce daidai; masu bincike da kuma malaman gona ka iya kin yarda. Aikin mai tattaunawar ne ya haska dukkanin sauran mahimman abubuwan da manoma za su iya amfani da su ga masu sauraro. Masu gabatar da tattaunawa na aiki a madadin masu sauraron su domin yada bayanai masu matukar mahimmanci iya iyawarsu. Wannan ya hada da tambayoyi masu tsauri, saboda bayanai masu amfani ka iya banbanta da abinda kwararre ya fada ko sakon da kwararre ke son aikawa. (A duba Kaidojin Aikin Jarida na F.A.I.R. domin masu Shirye-Shiryen Manoma musamman bangaren Mutunci)
7. Magance matsaloli
Me ya kamata mai gabatar da tattaunawa ya yi idan kwararre da yake tattaunawa da shi ya ci gaba da bada amsoshi da ba kai tsaye ba ko wadanda ba daidai ba?
- Ka sake salon tambayarka.
- Ka dakatar da daukar shirin sannan ka karfafawa kwararren guiwa don ya mayar da hankali wajen bada amsoshi kai tsaye. Ka yi masa bayanin cewa masu sauraro suna da bukatar su fahimci amsar da zai bayar a kan tambayar.
- Idan sauya salon tambayar bai yi aiki ba, Mai gabatar da tattaunawar zai iya gabatar da tambayar da daya daga cikin wadannan : 1) "Wannan gabar tana da mahimmanci, amma abinda nake ganin ya fi mahimmanci ga masu sauraronmu su sani shi ne …" Ko 2) "Yi hakuri, amma ina so na fahimci abin sosai …"
- Idan tattaunawar ta kai tsaye ce, ka karkare tattaunawar nan da nan domin kada ka batawa masu sauraro. Idan kuma nadar tattaunawar ake, ka tabbata ka tattauna da wani kwararren domin ya cike gibin bayanan.
Me masu gabatar da tattaunawa zasuyi a inda suka yi zargin cewa wani abu da kwararre ya fada zai iya zama ba daidai ba?
- Ka tabbatar da hakan sosai ta hanyar kara yin tambayoyi, kuma watakila ka iya tambayar hujja domin kare bayanan.
- Ka tambaya idan amsar gaskiya ce ko kuma ra’ayi na kashin kai kuma ka bincika daga baya daga wani tushen mai zaman kansa.
- Ka dakata har sai kwararren ya kammala, sannan cikin tausasawa ka gabatar da wani ra’ayi na daban da ka ji daga wani tushen kuma ka tambayi kwararren ya yi bayani.
- Cikin tausasawa ka tambayi kwarren: "Me kake tunani game da wannan ra’ayin da ya biyo baya game da wannan batun …?"
Yaya kwararre zai yi yayin da mai gabatarwa ya gabatar da bayanan noma ba daidai ba a yayin tattaunawa?
- Ka gyara masa cikin sauki da yanayi na tausasawa, kuma ka tuna cewa ba maganar waye ya fi wani ake yi ba, ana magana ne a kan aiki tare.
- Idan nadar tattaunawar ake yi, yaa kamata kwararre ya yi bayanin lamarin kuma ya gyarawa mai gabatarwa.
Me ya kamata kwararre ya yi a yayin da mai gabatarwa ya yi tambayar da ba shi ya kamata ya bada cikakkiyar amsarta ba?
- Ya kamata kwararre ya bayar da bayanai iyakacin iyawarsa, amma ya yi ko ta yi bayanin cewa ba shi ne ko ita ce ke da alhakin bada cikakkiyar amsar ba, kuma ya yi bayanin dalilin da yasa iyakacin iyawarsa kenan. Kwararre zai iya fadawa mai gabatar da tattaunawa sunan wani da zai iya bada cikakkiyar amsar tambayar.
- Ya kamata kwararru cikin tausasawa su yi magana a kan abinda ya rataya a wuyansu ba su faadi wasu bayanan daban ba, ko kuma su bayyanawa mai gabatarwa hukumar da abin ya shafa. Ya danganta da abinda ake magana a kai, za su iya bukatar cewa kada mai gabatar da tattaunawar ya nadi bayanan ko ya bayyana sunansu.
8. Kawar da al’adu marasa kyau da kuma sauran abubuwan da suke hana tattaunawa ta yi kyau
Za a iya samun matsaloli, da suka hada da al’adu da dabi’u, wadanda suke dakushe cikakkiyar sadarwa a yayin tattaunawa. Aikin mai gabatar da tattaunawa ne ya zama ya san wadannan al’adu da matsaloli, kuma a yayin da yake kiyaye su, ya yi kokarin samo hanyoyin samun bayanai ga masu sauraro.
9. Maza su tattauna da mata and mata su tattauna da maza
(Kuna a duba Yanda Zaka gamsar da Mata Manoma sosai)
Mai gabatarwa mace da kwarre namiji:
- Ya kamata mai gabatarwa ta yi shigar da ta dace ta mutunci.
- A zabi wajen da ya dace domin tattaunawar inda dukkansu za su iya yin magana ba tare da wata fargaba ba, kuma a samar da inda mace za ta iya barin wajen tattaunawar idan ta so yin hakan, ga misali, idan ta fahimci wata barazana daga wajen kwararre.
- Ki tabbatar da cewa kin tambaya kuma kin yi amfani da sunaye da adreshi daidai. Ga misali, ki kira mutane da irin su, Malam, ko Malama, ko Alhaj ko Hajiya, ko Shugaba, Ko Dakta, ko Farfesa, da sauransu. Ba ki da bukatar ki kara da cewa su kwararru ne. a maimakon haka, kawai sai ki fadi sunansu da lakabinsu da kuma watakila rawar da suke takawa ko aikinsu. Ta wannan hanyar za ki kaucewa bayar da yanayin da ke nuna cewa wadannan kwararru ne kuma manoma ba kwararru bane.
- Ki kaucewa nuna wariyar jinsi. Ga misali, kwarare zai iya bayar da misali da ya tashi kacokan daga abinda ya shafi zamantakewar gida, yana dauka cewa mai gabatarwa mace ba za ta fahimci batutuwan da suka shafi harkokin noma ba.
- Ki zamo kwararriya, kuma ki kula game da nuna wani yanayi da bai dace ba a fuska ko da jiki.
Mai gabatarwa namiji da kwararriya mace:
- Ka kaucewa nuna wariyar jinsi.
- Ka zamo kwararre, kuma ka kula game da nuna wani yanayi da bai dace ba a fuska ko da jiki.
- Ka bada tazara tsakaninka da kwararriya kamar yadda al’ada ta tanada.
- Lallai ka zabi gudanar da tattaunawar da rana.
- Ka yi shiga ta kamala da mutunci.
- Ka kaucewa gabatar da mace ta hanyar kiranta da wata alakarta da namiji (mahaifiyar, matar, da sauransu) ko kiranta da yanayin surarta (misali, "mai jan hankali"). A maimakon haka, kawai dai ka kira su da sunayensu da kuma lakabinsu, kamar yadda za ka gabatar da namiji.
- Ka yi la’akari da matsayin kwararriya na kwarewa kuma ka bata irin girman da za ka bawa namiji.
10. Ka kulla alaka
- A gaba, amincin da ke kulluwa ta hanyar kasancewa da tsayawa a kan lokaci (ga bangarorin biyu), kuma mai gabatar da tattaunawar ya ci gabada sanar da wanda aka tattauna da shi lokacin da za a yada tattaunawar kan haifar da alaka mai karfi.
- Ya kamata mai gabatar da tattaunawa ya tunatar da kwararre don ya saurari shirin a lokacin da ake yada shi, ka bukaci jin ta bakinsu, kuma ku tattauna bangarorin shirin don magance abubuwan da suka taso.
- Kasancewa cikin tuntubar juna a kai a kai zai taimaka wajen dorewar alaka, da kaucewa nuna cewa amfanin kwararre kawai shine lokacin da aka bukaceshi don tattaunawa. Ka sanya kwararre a cikin nasarar da shirin ya samu.
- Masu bada gudunmawa a kai a kai kan zamo abokan aiki, kuma akan shirya zama don tattaunawa game da shirye-shirye da maudu’ai.
- Ya kamata mai gabatar da tattaunawa ya yi bayanin cewa zai ko zata iya sake tuntubarsu domin wasu tattaunawar, kuma don haka za su iya neman cikakkun bayanan tuntuba.
- Zai yi kyau a basu ‘yan kudade domin biyan kudin mota da kudin kiran waya, amma bai kamata a kalli wannan a matsayin an biyasu kasancewar da suka yi a cikin shirin ba.
- Ga masu bada gudunmawa a kai a kai, a yi la’akari da yin bita sau biyu a shekara da kuma shirya taruka.
- Ka shirya karbar sakonni da tambayoyi da bibiya da kuma tattaunawa a kan lokaci tare da masu bada gudunmawa a kai a kai.
A ina kuma zan iya sanain wani abu game da tattaunawa da kwararru?
Nectary, undated. The Do’s & Don’ts Of Subject Matter Expert Interviews. http://nectafy.com/subject-matter-expert-interviews/
Godiya
Gudunmuwa daka: Vijay Cuddeford, Manajan tantance ayyuka, Farm Radio International, and Sylvie Harrison, Shugaban Tawagar Cigaban Radio Craft, Farm Radio International. Da Karin gudunmuwa daka Doug Ward, kwamitin kololi, Farm Radio International; da David Mowbray, Baban mai bada shawara, Farm Radio International.
Tushen bayanai
Wadannan mutanen masu zuwa sun amsa tambayoyi, ta haka ne aka tattara abubuwa da dama domin wannan Jagoran mai gabatarwar:
Masu gabatarwa:
Sheila Chimphamba, Zodiak Broadcasting Station, Malawi;
James Gumbwa, Malawi Broadcasting Corporation, Malawi;
Izaak B. Mwacha, Radio Maria, Tanzania
Mohemedi Issa, Abood Media, Tanzania
John Mkapani, Nkhotakota Community Radio Station, Malawi
Gideon Kwame Sarkodie Osei, ADARS FM, Ghana
Koleta Makulwa, Sahara Media, Tanzania
Adongo Sarah, Mega FM, Uganda
Mubiru Ali, Radio Simba, Uganda
Oumarou Sidibe, RTB2/Bobo, Burkina Faso
Koloma Irène Sayon, Radio Kafo-Kan, Mali
Samuel T. Sawadogo, Radio Manegda, Burkina Faso
Malaman gona, masu bincike, da sauransu:
Saulosi Kachitsa, Ministry of Transport and Public Works, Malawi
Esnarth Nyirenda, Department of Agricultural Research Services, Malawi
Fulla Yassin, Longido District Council, Tanzania
Danley Colecraft Aidoo, University of Ghana, Legon
Paschal Atengdem, University of Ghana, Legon-Accra.
Stella Aber, World Vision, Uganda
Philip Chidawati, Malawi Milk Producers Association
John Msemo, Ministry of Agriculture Livestock and Fisheries, Tanzania
Tumwesige Julius, Africa 2000 Network, Uganda
Doris Dartey, National Media Commission, Ghana
Richard Bambara, ONG LVIA, Burkina Faso
Moussa Kone, Local Service of Animal Products (SLPIA), Bougouni, Mali
Kirkira wanan takadun ya samu gudunmuwar Canada’s International Development Research Centre (IDRC) ta karkashin Canadian International Food Security Research Fund (CIFSRF).
Wana aikin an dauki gudunar dashi ne daka gudunmuwar kudi da gwamnatin kasa Canada ta bayar ta hanyar ofishin ta na Harkokin Duniya na kasar Canada.
This resource was translated with support from The Rockefeller Foundation through its YieldWise intiative.